Connect with us

Uncategorized

Jami’ar Federal University of Lafia Ta Kori wani Dalibi da Yiwa Malaminsa Ciki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An ruwaito da cewa an kori wani dalibi na Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa daga karatunsa a makarantar saboda zargin kwanci da yiwa Malamarsa Ciki.

An bayyana da cewa dalibin da aka kora yana karatun kimiyyar kwamfuta ne a makarantar kamin ya fuskanci kwamitin ladabtarwar Jami’ar wanda a karshe suka kore shi bayan zarginsa da laifin.

Kwamitin a bayaninsu sun gabatar da cewa halin dalibin na yiwa malamarsa ciki zai iya lalatar da girma da mutuncin cibiyar.

An kara da cewa halin a haka ya najasa da rusa mutunci malamar tare da yin watsi da ka’idojin da ke banbanta mu’amalar malamai da daliban Jami’a.

Kodayake, wasu mutane da suka mayar da martani akan lamarin sun yi Allah wadai da matakin da hukuncin da kungiyar kwamitin jami’ar ta yanke, sun yi lura da cewa babu wani abin matsala a yin soyayya tsakanin dalibi da malaminsa musanman idan dukansu magabata ne.

Yawancin mutane da suka kafa baki kan zancen sun yi Allah wadai da matakin girmama kai ga malami da kuma ka’idojin da ke tsara malami a kan mu’amala da ɗalibai a jami’o’in kasar.

Haka kazalika dalibin, bayan da ya karbi wasikar korarsa, ya bayyana cewa hukuncin da aka yanka masa bai daidaita ba, da cewa ai bai dauki matakin da son kansa ba.

A cikin bayaninsa kan abin da ya faru tsakaninsu, ya ce malamar ce ta nemeshi da yayi kwanci da ita. Ya kara da cewa ya gaza iya yin watsi da bukatan nata bayan da ta nuna masa da alamar munanan hukunci idan yaki faranta mata zuciyarta kan bukatar. “Ba shakka, malamar da kanta kyakkyawa ce,” inji Dalibin.