Connect with us

Labaran Najeriya

Kungiyoyi Sun Mamaye Birnin Tarayya Da Zanga-Zanga a Yau (karanta dalili)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Laraba, 27 ga watan Nuwamba, Kungiyoyin fararen hula a halin yanzu suna mamaye birnin tarayyyar Najeriya, Abuja, don nuna rashin amincewarsu da yunkurin gabatar da Dokar Kalaman Kiyayya, wadda a turance aka kira ‘Social Media Bills’, da kuma nuna bacin ransu da ci gaba da tsare wanda ya gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore da gwamnatin kasar ta yi.

Naija News ta fahimci cewa Masu zanga-zangar sun tari kofar shiga majalisar dokokin kasar ne a Abuja.

Ka tuna Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a wata sanarwa da Naija News Hausa ta bayar makoni biyu da suka gabata, tayi Allah wadai da kudirin da majalisar dokoki ke gabatarwa na kudurin kisa ta hanyar rataye ga masu yada kalaman kiyayya, wadda Sanata Sabi Abdullahi ya gabatar.

PDP sun lura a cikin nuna rashin amincewarsu da cewa idan har aka tabbatar da wannan dokar kisa ga masu kalaman kiyayyar, lallai dokar zai raunana tsarin mulki da dokokin kasar, zai lalata tsarin dimokiradiyya, da kuma dakile ‘yancin’ yan kasa da kuma haifar da mummunan son kai a Najeriya.

Haka kazalika Naija News ta ruwaito a baya da cewa Kungiyar Amnesty International ta zargi Shugaba Buhari da tsoratar da ‘Yan Najeriya

Kungiyar a wata sanarwa ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da yin amfani da jami’an tsaro da kuma bangaren shari’a don tsananta wa ‘yan Najeriya.

Kalli Hotunan Masu Zanga-Zangar a Kasa;