Connect with us

Uncategorized

Sabuwar Labari: Gwamnati ta Bude Rijistar Masu Laifin Jima’i Hadi da Fyaden Dole

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Litinin ta bayyana bude sabuwar rajistar masu aikata laifin fyade ga wadanda abin ya shafa da kuma sauran jama’a don bayar da rahoton aikata laifin fyade.

Rijistar wacce za ta kunshi sunaye da hotunan mutanen da aka kame da laifin fyade a cikin kasar wani bangare ne na dakile cin zarafin mata a Najeriya, bisa fahimtar Naija News.

Ka tuna a baya wannan kamfanin dilancin labarai ta ruwaito da cewa Jami’a Tsaro sun kame wani Tsoho Mai Shekaru 72 da ke yiwa Daliban Makarantar Sakandiri Fyade.

Naija News Hausa ta sanar da wani Tsoho da aka kame da ke yiwa kananan ‘yan makarantan Sakandiri biyu fyade a yankin Osogbo ta Jihar Osun.

An bayyana da cewa tsohon, mai shekaru 72 da haifuwa na kwanci kusan kullum da ‘yan makarantan sakandiri da ke a makarantar, da cewa ‘yan matan kan fita ne daga ajinsu a lokacin da sauran ‘yan makaranta ke cikin koyaswa, su kuma kara gaba zuwa gidan tsohon kullum don kwanci da shi.