Uncategorized
An Nada Sabbin Shugabannan Majalisar Dokokki A Jihar Taraba
A ranar Litini, 2 ga watan Disamba 2019, Mista Joseph Albasu Kunini da Alh Hamman Adama Abdulahi sun bayyana a matsayin sabon Kakaki da kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba.
Naija News Hausa ta fahimci cewa an zabi Kunini da Abdulahi ne ga matsayin a bayan da tsohon Kakakin majalisar, Habila Peter Diah ya yi murabus daga mukamin nasa a daren ranar Lahadi din da ta wuce.
Tsohon Kakakin Majalisar, Habila ya fada da cewa ya yanke shawarar murabus dinsa ne a kan wasu dalilai na sirri wanda ya ki bayyana wa.
Dan Majalisar wanda ke wakilcin mazabar Zing, Mista Bonzana Kizito ne ya zabi Kunini, sai kuma Ahmed Jedua na mazabar Gyembu shima ya amince da hakan a karo ta biyu.
Abdulahi kuma wanda ke wakiltar mazabar jihar biyu ya sami goyon baya da nadi daga Alh Bashir Muhammad, bisa rahoton da jaridar Sun ta bayar.
A yayin da ake bikin nadin, Kunini ya ce ya yi matukar farin ciki da aka iske shi da cancanta a majalisar, ya kuma yi alkawarin yin adalci da daidaitawa a rikon mukamin.
“Na gode da wannan amincewa. Ina tabbatar muku cewa zanyi amfani dashi don matsakaici ga bauta wa Allah da kuma cika burin ?an adam. Na gode da wannan gatan.”