Connect with us

Uncategorized

Dan Majalisar Wakilai a Jihar Kwara, Saidu Rufai Ya Mutu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A cewar wata rahoto da aka bayar daga kamfanin dilancin labarai ta Vanguard, dan majalisar wakilai a jihar Kwara, wanda ke wakilcin mazabar Patigi a zauren majalisar dokoki na 9 na jihar Kwara, Hon. Ahmed Saidu Rufai ya mutu.

Wannan sanarwan ya fito ne a kunshe a cikin sanarwar manema labarai wanda Mataimakin Musamman a kafofin watsa labarai ga dan majalisar, kakakin yada yawun majalisar Wakilai ta Jihar Kwara, Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi ya bayar.

Sanarwar ta ce;

“Hadi da matukar raha tare da mika wuya ga yardar Allah Madaukakin Sarki, muna sanar da rasuwar abokin aikinmu, Hon. Ahmed Saidu Rufai mai wakiltar mazabar Patigi ”.

“Wannan wani lamari ce wanda bamu zata ba da kuma ya jefa mu cikin wani mummunan hali, amma abin takaici, Madaukakin Sarki ya hana mu ikon juya irin wannan lamari da ya faru”, in ji Danladi.

“Yayin da muke kokawa da rayuwa tare da wannan mummunan al’amari da kuma yanayin da ake a ciki, muna rokon Allah cikin rahamarSa ya gafarta masa kurakuran sa, ya baiwa iyalan sa, majalisa ta 9, Patigi Emirate, abokan arziki na tarayya kuma da jihar Kwara baki daya, ƙarfin yin hakuri da amince da wannan al’amari da ya riga ya faru.”

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Hon. Ahmed Saidu Rufai ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin da safiyar yau kuma za a yi hidimar Jannazah na marigayin dan majalisar ne a yau jim kadam a harabar gidansu da ke a Patigi.