Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Hotuna da Takaitaccen Labarin Rayuwar Bilkisu Shema

Published

on

A wannan karamar hirar, Naija News Hausa na gabatar maku da daya daga cikin ‘yan mata da suka yi saurin tashe wajen shirin fina-finai na Hausa a karkashin kungiyar ‘yan fim da aka fi san da Kannywood, mai suna Bilkisu Shema.

Kyakkyawa da kuma shahararriyar, Bilkisu asalinta ‘yar Jihar Katsina ce. an haifi Bilikisu Shema ne a ranar 28 ga Watan Yuli a shekarar 1994.


Fitacciyar, Shema ta fara karatun ta na firamari ne a makarantar Isa Kaita College of Education, bayan nan ta shiga sekandari a Government Day Secondary School Dutsin-Ma.

Naija News Hausa ta gaza da samun tabbacin karatun babban jami’ar jarumar a wannan lokaci, idan hakan ya samu, zasu sami karin bayani.

Shema dai a cikin tashe a fagen fim a wannan lokaci, ita ce matashiyar jaruma wadda tauraronta yake haskawa.

Sanadiyar Haskawar Tauraron Bilikisu Shema:

‘Tabbatacce Al’amari’, wannan fim shi ne wanda ya sanya wannan jaruma darewa matsayi na daya a cikin jarumai mata a kannywood domin ta tsaga a tsakiyar gogaggu ta kuwa nuna gwaninta.

Kasancewar labarin fim din kusan a kanta yake, hakan ya bata damar taka rawarta har da tsalle. Domin mafiya yawan wadanda suka kalli shirin maganar ta kawai suke yi ba ta sauran jaruman ba.

A wata Hira Bilkisu ta shaida cewa tun bayan da tayi fim din farko taso tayi aure domin har ta daina karbar aiki, amma Allah cikin ikonsa bai nufi yin auren ba, duk dai bata sanar da dalilin da ya hana yin auren ba.


Yan mata da samari na fuskantar kalu bale da yawa daga ciki da wajen masana’antar fina-finai a kokarin su na tabbatar da burin su na zama manyan taurari, amma Bilkisu tun bayan tabbataccen Al’amari Ali Nuhu ya saka ta a wani Sallamar so, sai kuma finafinai irinsu Dawood, Ranah da dai sauransu wanda yanzu haka suna hanya basu fito ba,
Ita ce Wadda aka shirya zata fito a cikin fim din Mansoor sai ta makara ba ta zo da wuri ba har aka canja ta da wata.