Connect with us

Uncategorized

Mahara Da Bindiga Sun Sace ‘Yan Sanda Biyu A Jihar Adamawa

Published

on

at

Alhaji Ahmadu Dahiru, Shugaban Hukumar Kula da Canji, karamar hukumar Mubi ta kudu a Adamawa, ranar Asabar ya ce wadanda ake zargi sun sace wasu ‘yan sanda biyu sun kuma sace mutane bakwai a karkarar.

Bisa hirar Dahiru da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Gyela, ya ce; lamarin ya faru ne a kan hanyar Mubi zuwa Gyela, a ranar Talatar da ta gabata.

“Masu satar mutane suna tsoratar da kuma tsananta wa al’ummominmu a kullayomi, suna satar mutane da gangan a dare da rana. Sun kashe jami’an tsaro biyu a ranar Talatar da ta gabata wadanda suka yi sintiri a kan hanyar Mubi da Gyela.”

“A haka da nike magana da ku, kwanaki uku da suka gabata sun sace mutane biyar a Kwaja da biyu kuma a ?auyen Sauda,” in ji Dahiru.”

Ya bayyana da cewa, barayin sun yi ta tururuwa ne a saman wasu tsaunuka kusa a iyakar Najeriya da Kamaru.

Dahiru ya kara da cewa, al’ummomin sun yi asarar miliyoyin nairori ga masu garkuwa a yayin neman kubutar da wadanda aka sace daga hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguruje ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura wata rundunar jami’an tsaro don magance matsalar a yankin.

Ya kuwa yi kira ga jama’ar jihar da su kai rahoton duk wani alamun hari ko shigar ‘yan garkuwa da suka gane da shi zuwa ofishin tsaro mafi kusa.