Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Kadamar Da Bude Sabon Makarantar Jami’ar Sufuri A Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya ya bayyana da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya halarci bikin bude makarantar jami’ar sufuri a Daura.

Ka tuna cewa Daura a jihar Katsina ita ce garin shugaba Buhari.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shugaban ya isa Daura ne da yammacin ranar Juma’a, a bayan ya halarci taron kolin kungiyar kasashen waje na fitar da Gas a Malabo, a karkarar Guinea

Shugaba Buhari ya isa Filin jirgin saman kasa ta Umaru Musa Yar’Adua da misalin karfe 4.20 na maraice, a inda ya samu marabta daga gwamna Aminu Masari.

Shugaban kasa, wanda ke ziyarar aiki na kwanaki biyar a jihar, a yau Litini zai halarci bikin rantsar da Jami’ar sufur ta Daura, a yayi da zai karasa zuwa Kwanar Gwante, a hanyar Shargalle, wanda ke kan titin Kano-Daura.

“Kwalejin na musamman, wacce CCECC Nigeria Ltd za ta gina, za ta mai da hankali ne kan bincike da bunkasar babban bangare da kan sufuri.

Naija News Hausa ta kula da cewa Shugaban zai tashi daga Daura ranar Talata zuwa Kaduna.”