Connect with us

Uncategorized

Hukumar EFCC Ta Dafe Wani Tsohon Kansila A Karamar Hukumar Jihar Kwara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani tsohon kansila a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, Samuel Opeyemi Adeojo, ya fada hannun hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati.

Hukumar ta kama Adeojo ne da zargin zama jagoran wata satar motoci daga masu dilalan motoci ta hanyar zamba a matsayin masu siye na gaske.

Har zuwa lokacin da aka kama shi kwanan nan, hukumar ta EFCC ta dade tana kokarin neman kaman shi bayan da aka gabatar da kararraki game da ayyukan ta’addancin da zambansa tare da rukunin da yake sata da su, a wata karar daga Ofishin hukumar EFCC ta Ibadan.

Naija News Hausa ta fahimci cewa Fiye da lokuta uku aka gane shi hadi da zargin satar mota.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa dan majalisar wakilai a jihar Kwara, wanda ke wakilcin mazabar Patigi a zauren majalisar dokoki na 9 na jihar Kwara, Hon. Ahmed Saidu Rufai ya mutu.

Wannan sanarwan ya fito ne a kunshe a cikin sanarwar manema labarai wanda Mataimakin Musamman a kafofin watsa labarai ga dan majalisar, kakakin yada yawun majalisar Wakilai ta Jihar Kwara, Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi ya bayar.