Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 4 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 4 ga Watan Disamba, 2019

1. Rufewar kan iyaka: PPPRA Sun Karyata Shugaba Buhari Kan Amfanin Da Man Fetur a Kasa

Babban Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (PPPRA) ta karyace zance da ikirarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi game da yawan man da kasar ta samu ta hanyar rufe iyakar.

Naija News ta samu labarin cewa shugaban a yayin karban tawagar kungiyar dattawan jihar Katsina a garinsa Daura ya bayyana cewa, yawan diba da amfani da man fetur a kasar ya ragu sama da kashi 30 cikin 100 tun lokacin da aka rufe kan iyaka da makwabtan kasashe, yana mai nuni da cewa tun a baya akwai yawaitar zuba da amfani da man kasar. Ya kuma ce matakin da gwamnatin sa ta dauka kan yanayin zai ceci kasar biliyoyin nairori kan kudaden shigo da kaya.

2. DSS ta Bayyana Wata Sabuwar Shiri Na Kawo Damuwa A Najeriya

Ma’aikatar Tsaro ta kasa (DSS) a ranar Talata ta bayyana sabbin makircin da wasu kungiyoyi ke yi na jefa Najeriya cikin tashin hankali da aiwatar da zanga-zanga.

Hakan ya bayyana ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar.

3. Gwamnan PDP Ya Bayyana Goyon Baya Ga Buhari Kan rufe Shingen Kasar

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, a ranar Litinin, ya ba da cikakken goyon bayansa ga matakin Shugaba Muhammadu Buhari na rufe iyakokin kasar.

Umahi ya bayyana matsayin sa ne kan zancen a yayin makon bude Babban Bankin Kasa, a filin wasa na Onueke da ke karamar Hukumar Ezza ta Kudu a jihar.

4. Biafra: ‘Yan Sanda Sun Bayyana Kudurin Kamun Lauyan Nnamdi Kanu

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambra ta bayyana tabbacin neman kamun Ifeanyi Ejiofor, Lauya ga shugaban kungiyar‘ Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

A ranar Talata da ta wuce ne Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra, CP John Abang ya ba da sanarwar cewa, suna neman kamun lauyan gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra.

5. Saraki Ya Kalubalanci EFCC A Yayin Da Kotu Ta ba da Umarnin Sadaukar da Gidajen sa Ga Gwamnati

Tsohon shugaban majalisar dattijai na Najeriya Dr. Bukola Saraki ya bayyana umarnin da aka bayar na karbo kadarorin sa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, a matsayin cin mutuncin tsarin kotun da kuma keta dokar hana fita ta babban kotun tarayya da ke Abuja.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ba da umarnin cewa Saraki ya sadaukar da wasu gidajensa guda biyu a Ilorin sakamakon wata takaddar da hukumar EFCC ta gabatar akansa.

6. Gwamna Yahaya Bello ya Nemi Ma’aikatansa Da Su Nuna Masa Sakamakon Zaben Mazabarsu

Gwamnan jihar Kogi, Mista Yahaya Bello ya ba da sanarwar ka’idoji da kawai zai yi amfani da shi wajen zabin sabbin kwamitocinsa na siyasa wadanda za su yi aiki tare da shi a shekaru hudu masu zuwa.

Naija News ta tuno da cewa Gwamnan ya kori duk zababbun ma’aikatansa da bude sabon filin daukar sabbin ma’aikata.

7. Shugaba Buhari Ya Aika da Jerin Sabbin Shugabbanin Kula da Hidimar Hajji a Majalisa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen sabbin Shugabannai da membobin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ga Shugaban Majalisar Dattawa don tabbatarwa.

Hakan ya bayyana ne a cikin wata wasika da ya aika wa Majalisar Dattawa, wacce kamfanin dilancin labarai ta PRNigeria ta karba, Shugaba Buhari ya rubuta cewa:

“Bisa ga sashi na 3 (2) na Dokar Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) 2006, Ina mai farin cikin mikawa da neman tabbaci daga majalisar dattawa kan wadannan sunayen da aka zaba don matsayin Shugaba da membobin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa.”

8. Kada Ku Bawa Buhari Rancen Kudi – Inji Cif Olabode

Cif Olabode George, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ya yi kira ga kasashen waje da kar su bai wa Shugaba Muhammadu Buhari rancen kudi da yake bukata.

Mista George ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani game da shirin rancen dala biliiyan $29.96 na 2016-2018 da Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa saboda dubawa da amincewarsa.

“kasashen turai za su yi dariya da ba’a ga Najeriya saboda karbar irin wadanan bashi, saboda ya koka da yadda ake asarar kudaden kasar ta hanyar gudanar da yauka.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa