Connect with us

Uncategorized

Rikici Ta Barke Tsakanin Yarbawa Da Hausa a Jihar Osun

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

An yi asarar rayuka uku a cikin wata rikicin da ya shafi wasu matasa na Hausawa da kuma ‘yan asalin kauyen Iyere da ke karamar Hukumar Atakumosa ta Yamma a jihar Osun a ranar Litinin din da ta gabata.

Kodashike dai sanadiyar da ya haifar da rikicin baya a sane lokacin hada wannan rahoton, amma wakilinmu yada labarai da ya karbi rahoton ya samu labarin cewa a yayin wannan rikici, reshen kasuwannin da ya shafi Hausawa da Fulani ya kone duk da wuta.

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Osun ta bayyana da cewa mutum daya ne kadai aka rasa cikin rikicin.

Wani mazaunin Igila, wata kauye da ke kusa da Iyere, Olaide Agboola, yayin zantawa da manema labarai, ya ce mazauna Igila sun sami labarin rikicin da ya faru a Iyere ne da tsakar dare lokacin da wasu mutane da suka tsere daga wurin tashin hankalin suka shiga ƙauyen tasu.

Agboola ya ce daga bayanin da suka bayar, wani mutumi, Fulani da har yanzu ba a san asalinsa ba yana fada ne da wani Ba’Hausa a yayin da kuma wani dan asalin garin Iyere, wanda ya mallaki wani shago da ke kusa da shi ya sa baki don hana batun ya kara tabarbarewa.

“Abin takaici, An kashe dan Bayarben da ke kokarin neman sulhu tsakanin Bahaushen da Bafillacen. Wasu mazauna garin, a kokarin neman ramuwar gayya, su kuma suka kashe wasu matasan Hausawa biyu nan take. Wannan ne ya jawo rikice-rikicen. Kuma fadar ya dauki tsawon dukan dare.” inji Shi.

“Shagunan da ke a bakin Titunan duk an kone. Kayayyakin da suka kai miliyoyin nairori duk anyi asararsu a rikicin. ‘Yan sanda da sojoji kuma sun isa garin kuma, a yanzu haka komi ya kwanta” in ji Agboola.

Sarkin Igila, Oba Samuel Falaye, ya shaida wa manema labarai cewa, daga rahotannin da aka bashi game da zancen, lallai an yi asarar rayuka, yayin da kuma an kone da lallace kasuwar.