Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Motar Yakin Sojoji Ta Farko da aka Kera a Najeriya (Kalli Hotuna)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata a jihar Kaduna ya kaddamar da Motar Yaki na Sojoji da aka kera a karon farko a Najeriya.

Motar da aka kera wacce ke da lambar suna ‘Ezugwu, za a yi amfani da ita wajen ayyukan sojin ne a yankin arewa maso gabas.

Naija News Hausa ta samu fahimtar cewa Kamfanin Masana’antu na Rundunar Tsaron Najeriya (Defence Industrial Corporation of Nigeria) wacce ke a Kaduna ne ta kera shi.

A yayin jawabi a wajen taron, Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da damar don yin ta’aziya ga dukkanin sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, tare da gode masu kan kokarinsu da jajircewarsu wajen ganin kasar ta zauna lafiya.

“Wannan gwamnatin na sane da cewa ayyukan sojojin sun zo da wasu sakamako masu mahimmanci, tare da wasu jarumai da suka samu raunuka daban-daban.”

“Ina sake aika da sakon ta’aziyata ga wadanda suka yi sadaukarwa matuka a kokarin tabbatar da kare kasar nan. Ina mai fatan Allah yasa su huta lafiya.”

Shugaban ya kara da cewa “Ina kira ga sojojinmu da su ci gaba da bin ka’idodin aikinsu tare da kiyaye ka’idodin hadi da tabbatar da cewa ana inganta da mutunta ‘yancin bil adama da dokokin kasa da kasa kan ayyukan soja,”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari Ya Bar Daura Zuwa Jihar Kaduna bayan kammala ziyarar kadamarwa ta aiki ta kwanaki biyar.