Connect with us

Labaran Najeriya

‘Yar Shugaba Muhammadu Buhari Ta Karshe Karatun Ta A Burtaniya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A’isha (Jnr), daya daga cikin ‘ya’yan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Aisha Buhari ta kamala karatun digiri a jami’a da ke a Burtaniya (UK).

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne ta bayyana wannan labarin a cikin wani sakon kafofin sadarwa ta Twitter wadda ta rabar a ranar Talata da yamma inda ta gode wa dangi, abokai, da kuma masu kyakkyawan tunanin bikin tare da dangin ta duka.

Naija News ta fahimci diyar shugaban, mai suna Aisha ta kammala karatun ta da lambar girmamawa ta farko ne.

Duba hotuna a kasa: