Connect with us

Uncategorized

2023: Hanya Daya Kacal Da Kudu Maso Gabashin Kasar Zata Iya Lashe Kujerar Shugaban Kasa – Okorocha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanata da ke wakilcin yankin kudu maso gabas ta Najeriya a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha ya ce yankin kudu maso gabas zata iya samun kujerar shugabancin kasar Najeriya ne a 2023 idan suka hada hannu da arewa da sauran bangarorin siyasar kasar.

Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba da ta wuce.

Okorocha a cikin bayanin sa ya ce Najeriya na bukatar shugaba ne da zai ci gaba da kokarin hada kan ‘yan kasar, samar da ayyukan yi da kuma bada tabbacin tsaro.

“Iyamirai a kadaicin su ba za su iya samar da shugaban ƙasa ba. Akwai bukatar su hanzarta da neman hadin kai da tallafi daga Arewa da sauran sassan yankin, hakan kawai zai fi kyau ga cinma gurinsu da wuri.” Inji Okorocha.

“Na san cewa, za mu kai ga cinma wannan lokacin a nan gaba, musanman idan wanda ya zama shugaban kasa ba wai an zabe shi bane don nuna kabilanci ko addini. Muddin muka ci gaba da inganta kabilanci da addini, to lallai bamu ba abin da ya dace.”

“Idan zaku yi la’akarin siyasar kasar a yau, kowa ya zura ido ga Arewa saboda tana da manyan kuri’a don tantance wanda zai zama shugaban Najeriya,” in ji shi.

“Wani abin da tabbas na sani da Arewa, musamman kasar musulunci, shi ne cewa musulmin kirki mutumin kirki ne wanda ya yi imani da gaskiya, adalci da kuma hadin kai.”

“Wannan kadai shine abin da ake bukata da fata a duk wani mai son tsayawa takara daga yankin kudancin kasar. Arewa zata iya sadaukarwa don tabbatar da adalci da kuma gujewa nuna bambance-bambancen kabila da addini, a duban cewa tunda Arewa tayi shugabancin kasar, sai wani daga Kudu shima ya dana da zama shugaban kasa na gaba,” in ji shi.