Connect with us

Uncategorized

Majalisar Dattijai Ba za ta Zartar da Dokar Kalaman Kiyayya Ba – Shugaban Majalisa

Published

on

Shugaban majalisar dattijai ta Najeriya, Ahmed Lawan ya ce zauren majalisun dokokin kasar ba za su zartar da dokar yada kalaman kiyayya ba.

Wannan zancen ya biyo bayan koke-koke da zanga-zangar da aka yi kan kudirin kalaman kiyayya wadda Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, mai wakilcin APC a jihar Neja ya gabatar.

Ku tuna, kamar yadda Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce, ‘Da Lai Mohammed ya mutu ko idan da a ce an kafa dokar kisa kan kalamun kiyayya tun wa’adin Jonathan’.

Abaribe ya mayar da martani game da dokar mutuwa ta hanyar ratayewa wanda ke a kunshe cikin wata sabuwar tsarin da Majalisar Dattawa ke kokarin kafawa.

Abaribe a cikin yada yawunsa ya haɗu da wasu ‘yan Najeriyar don ƙin amincewa da dokar.

Yace; “Idan da an riga an zartar da irin wannan dokar a lokacin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed a yanzu ya mutu ko.”