Connect with us

Uncategorized

APC: Kotun Ta Saka Orji Uzor Kalu Ga Shekaru 12 a Gidan Yari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari a hukuncin babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Alhamis.

Sanatan da ke wakiltar mazabar Arewacin Abia, Kalu, an same shi ne da tabbacin laifuka a kan dukkan tuhume-tuhume 39 da aka gabatar a kansa.

Naija News ta gane cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta dahe Sanatan ne da laifin almundahana da Naira biliyan N7.65 yayin da yake rike da mukamin gwamnan jihar Abia tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

An gurfanar da Kalu ne tare da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited hadi da tsohon darektan kudi, Ude Udeogu.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babbar Kotun Tarayya da ke a Legas, a cikin hukuncin da ta yanke, ta umarci Gwamnatin Najeriya ta kwato dukkan kudaden fansho da duk tsoffin gwamnoni suka karba da a yanzu duk suna zaman Sanatoci da Ministocin Tarayyar Najeriya.

Haka kuma Kotun ta umarci babban alkalin tarayya da Ministan shari’a, Mista Abubakar Malami (SAN), da ya kalubalanci gaskiyar dokar fensho na jihohi da ke baiwa tsoffin gwamnoni da sauran tsoffin jami’an gwamnati damar karban irin wadannan kudaden.