Connect with us

Uncategorized

Wani Ciyaman Na Jam’iyyar PDP A Filato, Yayi Murabus Da Matsayin Sa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na Filato Damishi Sango, ya yi murabus daga mukamin nasa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, wannan ya biyo ne bayan zargin cin hanci da rashawa da aka yi a kansa.

Da yake bayar da dalilan murabus din sa a taron manema labarai da ya yi, Sango ya ce rikicin da ke barazanar wanzuwar jam’iyya a jihar Filato na daga cikin dalilan da yasa yayi murabus da matsayin nasa.

Ya fada da cewa mataimakinsa, Amos Gombi, zai maye gurbinsa na mukamin shugaban jam’iyyar.

“Kun san cewa tun daga watan Afrilun wannan shekara, rikicin mai tsanani ya harzuka wannan yanki na babbar jam’iyyar mu, wanda ya yi barazana ga kasancewar jam’iyyar mu ta siyasa,” in ji Sango.

“Wannan ya biyo bayan dakatarwar da aka yi min ne tare da mataimakina a matsayin shugaban majalisa da mataimaki, ta hannun wasu mambobin kwamitin zartarwa a kan zarge-zargen makudan kudade da aka yi amfani da su a shirye-shiryen babban zaben kasar na shekarar 2019 a jihar.”

Ya kara da cewa kwamitin bincike ta Mark din da aka kafa basu same shi da wani laifi ba.

“Bayan janye tuhumar, bisa la’akari na da cewa akwai mummunan bakin jini a tsakanina da mafi yawan abokan aikina a kwamitin zartarwa, musamman kungiyar ta 16, da kuma yin hanyar samar da zaman lafiya a cikin jihar, ya kamata in janye daga mukamin nawa.” inji Sango.