Uncategorized
Hukumar DSS Sun Yi Koƙarin Sake Kamun Sowore Da Bakare
Bayanai da ke isa ga Naija News a yau safiyar Juma’a ya nuna da cewa jami’an ma’aikatar tsaro ta DSS sun yi kokarin sake kama Omoyele Sowore da Olawale Bakare.
Ku tuna da cewa su biyun an sake su ne kan beli daga hannun ‘yan sanda asirin ranar alhamis da yamma bayan hukuncin karar da kotu ta yanka.
Bisa rahoton da kamfanin dilancin labarai ta Sahara Reporters ta bayar wadda wakilinmu ya gano da ita, ta ce jami’an DSS sun kutsa kai ne a harabar kotun da safiyar Juma’a yayin da suke kokarin sake kama su biyun.
A cewar rahoton, jami’an DSS sun hana alkalin kotun, Mai shari’a Ijeoma Ojukwu zama a kujerarta, har da cin mutuncin wani dan jarida a cikin lamarin.
A yanzu haka dai takaddama tana gudana a cikin harabar kotun yayin da jami’an hukumar DSS suka ki barin Sowore da lauyoyinsa su fita da kotun.