Connect with us

Uncategorized

Kalli Jerin Suna Da Hotunan Tsofaffin Gwamnonin Najeriya Da Aka Jefa Gidan Yari Kan Cin Hanci Da Rashawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kimanin tsofaffin gwamnoni shida na Najeriya da kotu tayi masu shari’a kan cin hanci da rashawa da kuma yanke masu hukuncin shiga jaru.

Naija News ta ruwaito cewa Orji Uzor Kalu, wani tsohon gwamnan jihar Abia, kudu maso gabashin Najeriya da kuma shugaban gudanar da zabe a gidan majalisar dattijai, shine na farko akan jerin.

Ga jerin tsoffin gwamnoni shida waɗanda aka gane da cin hanci da rashawa da kuma aka jefa a Kurkuku:

1. Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia, kuma shugaban gudanar da zabe a gidan majalisar dattijai, shi ne na baya akan jerin kungiyar tsoffin gwamnonin da aka daure saboda cin hanci da rashawa. Naija News ta ruwaito da cewa Kotun tarayya da ke a Legas ta yanke wa Sanata Kalu hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari a ranar alhamis din da ta wuce, akan cin hanci da rashawa na kimanin biliyan N7.65bn, hadi da wasu hukunci da ya shafi jaru na shekaru 3 zuwa 5 a kan kararraki 27.

2. Jolly Nyame

An yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba, arewacin Najeriya, Jolly Nyame hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba. Bayan da aka same shi da aikata laifuka 27 cikin tuhume-tuhume 41 da ake zargin sa kan karkatar da kudaden jama’a.

3. James Bala Ngilari

An yanke wa wani tsohon gwamnan jihar Adamawa, arewacin Najeriya, Bala Ngilari hukuncin shekaru 5 a gidan yari a shekarar 2017 ba tare da wani zaɓin biyan tara ba, akan bayar da kwangila ba tare da bin tsari ba har na kimanin naira miliyan N167m.

4. Joshua Dariye

An yankewa wani tsohon gwamnan jihar Filato, arewacin Najeriya, Joshua Dariye hukuncin ɗaurin shekaru 14 a kurkuku bisa laifin keta amana da laifin cin amana da zaluncin jama’a a shekaru biyu. Dariye dan majalisar dattijai ne a shekarar 2018. An tuhume shi da almubazzaranci na naira biliyan 1 da miliyan 162 na ilimin muhalli, mallakar jiharsa. Daga baya aka rage hukuncinsa na zaman gidan yari zuwa shekaru 10.

5. Lucky Igbinedon

An yanke wa wani tsohon gwamnan jihar Edo, kudu-maso-kudancin Najeriya, Lucky Igbinedion daurin watanni shida a gidan yari a shekara ta 2008 saboda karbar kudi da yawansu ya kai biliyan 25. Tsohon gwamnan, duk da haka, ya samu wata yarjejeniya akan roko da ta sa shi biyan tarar Naira miliyan uku da rabi.

6. James Ibori

Wata kotun Landan ta yanke wa wani tsohon gwamnan jihar Delta, kudu maso gabashin Najeriya hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari saboda laifin zamba ta layin yanar gizo mai kimanin yawar kudi dala miliyan $250. Tsohon gwamnan tun daga lokacin ya kammala zamansa a kurkuku ya kuma dawo kasar Najeriya, inda ya samu babban marabta a cikin jiharsa.