Connect with us

Uncategorized

Malamin Arabi Ya Zalunci Wani Mutum Sama da Miliyan 3 Da Alkawarin Shigar Da Alqur’ani Akansa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ce ta kama wani Limami mai suna, Mallam Abdulrahim, a Kaduna saboda cin amanar wani mutumi mai suna Arc Mohammed Dewu, sama da yawar kudi Miliyan N3,024,000.

Wannan ya biyo ne bayan takardar kara wacce Arc Dewu ya wallafa da zargin cewa malamin a kwanakin baya a watan Oktoba na 2019, yayi masa zamba da karɓan kuɗaɗen bayan ya ce yana da iko mai tasiri na Kur’ani, hadi da Aljannu da yake aiki tare da su da zai iya sanya cikakkiyar Alƙur’ani a kansa.

Dewu ya bayar da cewa malamin da ake zargin ya sa shi ya sayi abubuwa kamar haka:

“Kwalban Turare guda biyu a N70,000; Gilashin turare ta musamman akan N160,000; Kwalban Turare guda ta musanman don maganin ciwon mahaifiyarsa a kan N550,000; Zafafan turare guda sittin (60) don kunna ayoyin Qur’ani da zasu shiga cikin kwakwalwarsa da karfin aljani akan kudi miliyan N1,680,000; Wayoyin Salula biyu da katin SIM a N20,000; Bokitin zuma Talatin”

A cewar Dewu, Malamin ya yaudare shi da cewa wadannan abubuwan za su taimaka masa wajen zuba ayoyin Alqur’ani zuwa kwakwalwarsa, watau kwakwalwar Dewu.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa An kama wani Malamin Almajirai da laifin yin Jima’i da  daliban sa.

Rukunin ‘Yan Sandan Najeriya ta Jihar Sokoto ta kama wani Malam Murtala Mode, malamin makarantar Almajirai a garin Arkillan Magaji na jihar Sokoto da zargin cewa yana yin jima’i da yara shida da yake koyar da su a Jihar.

Malamin da aka kama shi, a cikin bayanin sa ya ce”Makoma na ne, nikan yi shi ne don samun kudi”