Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 6 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 6 ga Watan Disamba, 2019

1. Kotun Ta Saka Orji Uzor Kalu Ga Shekaru 12 a Gidan Yari

An yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari a hukuncin babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Alhamis.

Sanatan da ke wakiltar mazabar Arewacin Abia an same shi ne da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume 39 da aka gabatar a kansa.

2. Kotu ta Ba da Umarnin Karshe Kan Neman Takarar na uku Ga Shugaba Buhari

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress, Charles Enya, wanda ya shigar da karar neman a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don bai wa Shugaba Muhammadu Buhari damar neman wa’adi na uku a karagar mulki ya janye karar.

Jigo a jam’iyyar ta APC a cikin wata sanarwa ya ce ficewar karar ya biyo ne don bada damar ci gaba da wasu bincike.

3. Kotu Ta Ba DSS Awanni 24 Don Sakin Sowore, Bakare

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar DSS da ta saki jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, da Olawale Bakare a cikin awanni 24.

Naija News ta fahimci cewa Mai shari’ar, Ijeoma Ojukwu, wadda ta ba da umarnin ta kuma bayar da tarar N100, 000 akan DSS kan jinkirin da hukumar tayi wajen sakin Sowore da Olawale Bakare.

4. Majalisar dattijan Najeriya ta zartar da kasafin kudin 2020

A ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba, Majalisar Dattawan Tarayya ta zartar da kudurin dokar kudi ta shekarar 2020, wanda ya karu daga jimillar kudi tiriliyan N10.33tn zuwa N10.6tn, fiye da yadda aka gabatar a da.

Wannan ya biyo bayan la’akari da zartawar rahoto da kwamitin majalisar suka bayar game da cancantar kudirin.

5. Kotu Ta Umurci Hukumar DSS Da Ta Mayar Da El-Zakzaky Ga Cibiyar Horon Al’umma

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta ba da umarni ga hukumar DSS da ta dauki shugaban IMN, kungiyar ci gaban Musulunci da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da uwargidansa Zeenat daga tsarewar ma’aikatarta zuwa cibiyar gyara halin al’umma ta jihar Kaduna.

Alkalin kotun ya bayyana da cewa yin hakan na da kyau don inganta da samun saukin saduwa da shi.

6. Ci Gaba Da Tsare Sowore, Halin Ta’addanci Ne – Soyinka ya gaya wa Buhari

Babban Marubuci a Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya fada wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ci gaba da tsare jagoran kungiyan zanga-zanga wacce aka fi sani da #RevolutionNow, Omoyele Sowore, wani halin cin zarafi da ta’addanci ne.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta umarci hukumar DSS ta saki Sowore da Olawale Bakare a tsakanin awanni 24.

7. Majalisar Wakilai Ta Tarayya Ta Zartar Da Kasafin Kudi Ta 2020

A yau Alhamis, 5 ga watan Disamba, Majalisar Wakilai ta Tarayya ta zartar da kudurin dokar kudi ta shekarar 2020, wanda ya karu daga jimillar kudi tiriliyan N10.33tn zuwa N10.6tn, fiye da yadda aka gabatar a da.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar ta gabatar da sabon adadi a yayin da ta gabatar da rahotonta game da kasafin kudin shekarar 2020 a ranar Laraba da ta wuce.

Wannan ya biyo bayan la’akari da zartawar rahoto da kwamitin majalisar suka bayar game da cancantar kudirin.

8. 2023: Hanya Daya Kacal Da Kudu Maso Gabashin Kasar Zata Iya Lashe Kujerar Shugaban Kasa – Okorocha

Sanata da ke wakilcin yankin kudu maso gabas ta Najeriya a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha ya ce yankin kudu maso gabas zata iya samun kujerar shugabancin kasar Najeriya ne a 2023 idan suka hada hannu da arewa da sauran bangarorin siyasar kasar.

Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba da ta wuce.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a Naija News Hausa