Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Na Ganawa Da Oshimhole, Manyan ‘Yan APC Don Hana Rushewar Jam’iyyar Bayan Wa’adinsa Ta 2

Published

on

Buhari Ya Zarta Da Manyan Shugabbanai A APC Kan Rikicin Da Ke Gudana a Jam’iyyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau jumma’a, 6 ga watan Disamba 2019 na ganawa da Shugaban Jam’iyyar APC kan neman zabe na kasa, Adams Oshiomhole kan rikicin da ke ta karatowa jam’iyyar da ke shugabanci.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Shugaba Buhari a ranar Alhamis ya gana da gwamnonin APC a Fadar Shugaban kasa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wannan dandali na labarai ta yanar gizo ta fahimci cewa gwamnonin jam’iyyar APC sun halarci taron ne a jagorancin Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, arewa maso-yammacin Najeriya.

Taron kuwa ta samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Shugaban Ma’aikata ga Shugaban, Mista Abba Kyari.

Koda yake, shugaban jam’iyyar APC na kasa da ake bukatar bayyanarsa a taron bai samu hallararta ba.

An tattaro cewa Oshiomhole a yau zai gana da Shugaba Buhari, tare da shugabannin jam’iyyar na kasa.

Wani babban jigo a jam’iyyar APC ya fada wa jaridar The Punch da cewa, “ganawar ta biyu wani bangare ne na kokarin kawar da rarrabuwar kawunan ‘yan jam’iyyar bayan wa’adin shugaba Buhari na biyu.

Wani abokin aiki da Oshiomhole ya bayyana cewa tsohon gwamnan, Oshiomhole, bai karbi gayyata kan taron jam’iyyar APC ba wacce ta gudana a ranar Alhamis, saboda haka bai kamata a yi tsammanin hallararsa ba a taron.

“Taro ne da gwamnonin APC suka yi don haka bai kamata shugaban jam’iyyar ya halarci taron ba. Gobe dai (Juma’a) zai jagoranci manyan shugabannin jihohi don ganawa da Shugaban kasar,” inji shi.

Naija News Hausa ta fahimci cewa wannan itace taron farko da shugaba Buhari zai yi da Ciyamomin jam’iyyar ta jiha tun bayan babban zaben 2019.