Connect with us

Uncategorized

Babachir da APC Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), reshen Adamawa, sun yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar.

Naija News ta ruwaito da cewa Shugaban Hukumar Zaben Kasa ta Jihar Adamawa (ADSIEC), Mallam Isa Shetima ya sanar bisa zabe cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe dukkanin zaben kananan hukumomin karamar hukuma 21 a zaben ranar Asabar a jihar Adamawa.

Shetima ya bayar da cewa hukumar ta riga ta sanar da sakamakon majalissar kananan hukumomi 226 a bayan karshe zaben, kuma za a basu takardun shaida na dawowar su akan jagoranci a wannan Litinin.

A yayin bayani akan zaben, Jam’iyyar APC ta bakin mai bada shawarwarita a kan sharia, Shagnah Pwamadi, ya bayyana zaben a matsayin “zaben da aka ci nasara da hadin kan hukumomin tsaror,” yana mai cewa wannan ne dalilin da ya sa APC tayi watsi da sakamakon zaben.”

Shagnah ya ce jam’iyyar za ta yi duk abin da ya dace akan doka don neman yancinta, “Zaben da aka gudanar cikakken abin kunya ne, mara jituwa da kasa da abin da ake kira zabe.” inji Shi.

“Wannan zabin ne wanda aka aiwatar karkashin tsoratarwa da tursasawa. Ba za mu amince da shi ba,” in ji Pwamaddi.

Hakanan kuma yayin mayar da martani game da zaben, wani jigo a APC, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir Lawan, a cikin wata sanarwa ya ce ba a gudanar da zaben a karamar hukumarsa (Hong) ba.

“Duk da tabbacin da gwamnan jihar Adamawa ya bayar cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar da adalci da gaskiya, amma ba a yi zaben a cikin Hong ba, ba zabe ko a cikin mazaba daya.” inji Babachir.

“Babu kayan zabe, babu kuma wani jami’in zabe da aka hanga a cikin karamar hukumar Hong har zuwa karfe hudu na yamma a ranar Asabar lokacin da na koma Yola.”

“Wannan mummunan cin mutuncin mutanenmu ne bisa lurar mu.  Mun yi tsammanin wannan gwamnatin da ta gudanar da zaben mai adalci da mafi kyau saboda da bai hau mulki ba idan gwamnatin tarayya ba ta ba INEC damar gudanar da zaben gaskiya da adalci ba a wancan babban zaben” in ji Babacir.