Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 9 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 9 ga Watan Disamba, 2019

1. Fadar Shugaban Kasa ta Mayar da Martani kan Sake Kame Sowore ta hannun DSS

A karshe fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga Tsananci da hukumar DSS suka wa Omoyele Sowore, jagoran neman juyin juya mulki.

Naija News ta ruwaito tun farko cewa hukumar DSS ta saki Sowore a daren ranar Alhamis bayan ya kwashe kwanaki 124 a tsare.

2. Sowore: Atiku Da Jam’iyyar PDP na Zancen Karya Don Bacin Hali Ga Shugaba Buhari da DSS – APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP da yada wasu bayanai na karya game da sake kame Omoyele Sowore da aka yi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, Ma’aikatar Tsaro ta kasa (DSS) a daren ranar Alhamis din da ta gabata ta saki Sowore bayan ya kwashe kwanaki 124 a tsare.

3. Bai Yiwuwa Mu yi Tsige ko bayyana kujerar Orji Uzor Kalu bude – Majalisar Dattijai

Majalisar dattijan Najeriya ta ce ba za ta ayyana kujerar Shugaban Whip din ta, Sanata Orji Uzor Kalu ba, duk da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoto a baya da cewa cewa, babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Alhamis, ta samu tsohon gwamnan jihar Abia da laifin dukan wasu tuhume-tuhume 39 da aka zarge shi da su.

4. Faduwar Mutum Ba Karshen Rayuwarsa ba, Buhari ya maida martani ga nasarar Anthony Joshua

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga nasarar Anthony Joshua a kan Andy Ruiz Jnr dan kasar Mexico a wani muhimmin hadewar danbe tsakanin su biyun har sau 12 a fada guda.

A wata sanarwa ranar Lahadi ta hannun mai bada shawara ta musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban, Femi Adesina, ya wallafa da cewa Buhari ya taya Joshua murnar sake dawo da nasararsa, musanman kyautukan da belitinsa da yake dauke da su a da.

5. Wasu Yan bindiga Sun Sace Firistocin Katolika guda biyu A Ondo

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wasu limaman cocin Katolika biyu a kan hanyar Owo-Benin a jihar Ondo.

Naija News ta fahimci cewa Malaman suna kan hanyarsu ne daga Awka, jihar Anambra hanyar zuwa Akure, babban birnin Ondo, don wata bikin aure a lokacin da aka sace su.

6. Biafra: Nnamdi Kanu Ya Bayyana Tabbacin Dalili Da Yasa Sowore Ke a Kurkuku

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce Omoyele Sowore, jagoran kungiyar zanga-zangar #RevolutionNow yana hannun jami’an Ma’aikatar tsaro ta Jiha (DSS) ne saboda ya gana da shi (Kanu).

Kanu ya yi wannan bayanin ne yayin wata gabatarwa da yayi a gidan Rediyon Biafra a ranar Lahadi, 8 ga Disamba, inda ya yi magana kan cin zarafin Sowore da jami’an DSS suka yi da kuma cin zarafin bil adama a Najeriya.

7. Babachir da APC Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Adamawa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), reshen Adamawa, sun yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar.

Naija News ta ruwaito da cewa Shugaban Hukumar Zaben Kasa ta Jihar Adamawa (ADSIEC), Mallam Isa Shetima ya sanar bisa zabe cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe dukkanin zaben kananan hukumomin karamar hukuma 21 a zaben ranar Asabar a jihar Adamawa.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a Naija News Hausa