Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Yobe Ya Dakatar da Wani Hakimi Kan Laifin Lalata Da Wani Yaro Dan Shekara 6

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ba da umarnin dakatar da shugaban gundumar Fannami, Lawan Mari daga karamar hukumar Bade saboda zargin yin lalata da wani yaro dan shekara shida.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Harkokin Cikin gida da Al’adu, Abdullahi Bego, ya ce gwamnan ya ba da umarnin gaugawa da a dakatar da shugaban gundumar.

Sanarwar ta ce:

“Mai martaba ya ba da umarnin a dauki matakan da suka dace na gudanarwa da kuma bin doka cikin hanzari don gudanar da bincike ta musanman tare da hukunta lamarin. “A sakamakon haka, an dakatar da hakimin ba tare da jinkiri ba akan matsayinsa a gundumar Fannami, Gashu, har sai ‘yan sanda sun gama bincike akan lamarin.”

“A haka an riga an bayar da wasikar dakatarwa ga hakimin daga hannun kansilan karamar hukumar Bade.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC ta kama wani Limami mai suna, Mallam Abdulrahim, a Kaduna saboda cin amanar wani mutumi mai suna Arc Mohammed Dewu, sama da yawar kudi Miliyan N3,024,000.

Wannan ya biyo ne bayan takardar kara wacce Arc Dewu ya wallafa da zargin cewa malamin a kwanakin baya a watan Oktoba na 2019, yayi masa zamba da karɓan kuɗaɗen bayan ya ce yana da iko mai tasiri na Kur’ani, hadi da Aljannu da yake aiki tare da su da zai iya sanya cikakkiyar Alƙur’ani a kansa.