Connect with us

Uncategorized

Zaben Kogi: Natasha Ta Gabatar Da Karar Rashin Amince Da Zaben Bello a Kotu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yar takarar kujerar gwamna a jihar Kogi a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna a ranar 16 ga Nuwamba 2019, Natasha Akpoti, ta tunkari kotun kolin zabukan gwamnoni kan sakamakon zaben.

A cikin takardarta, Barr. Akpoti ta shigar da kara a gaban kotun a ranar Asabar da daddare, na neman a soke zaben.

Ta sanya sunan wanda ya lashe zaben, Gwamna Yahaya Bello, da abokin karawarsa Edward Onoja, da Hukumar Gudanar da Zaben Kasa (INEC), hadi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wadanda take karar akai.

A cikin karar da Akpoti ta gabatar, ya bayyana da cewa zaben ya gudana ne da rashin daidaituwa tare da tashin hankali kuma a saboda haka, ta bukaci kotun ta nemi Bello da sauka daga kujerar sannan ta umarci INEC ta sake gudanar da sabon zabe.

Ta kara a cikin karar da cewa cire sunan ta daga wasu takardu na sakamakon zaben da aka yi, da kuma matakin rubuta sunanta da Biro a takardar sakamakon abu ne da bata amince da shi ba.

Naija News ta fahimci cewa Babban Lauya, Ola Olanipekun, (SAN) ne ya wakilci Akpoti a gabatar da karar.