Connect with us

Labaran Siyasa

Gwamnan Adamawa, Fintiri Ya Hana Ciyamomin Kananan Hukumomi Tafiye-Tafiye

Published

on

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya gargadi shugabannin kananan hukumomi a jihar daga tafiye-tafiyen da basu kamata ba. Gwamnan na mai cewa gwamnatin sa “ba za ta amince da irin wannan dabi’a ba inda shugaba zai yi watsi da aikin jami’in nasa ba tare da dalili ba.”

Fintiri ya tuhumi sabbin shugabannin da aka nada da samar da rabon dimokiradiyya ga jama’arsu tare da hana su tafiye-tafiye marasa galihu daga kananan hukumominsu, sai dai idan tafiyar ya zama dole.

Gwamnan ya gargade su da su ci gaba da kasancewa a kananan hukumominsu tare da fuskantar shugabanci da kuma daina saka kansu a kan abubuwan da suka zama dole garesu wanda ba za su kara daraja ga mutane ba. yana mai cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen cika dukkanin alkawuran da ta yi wa jama’a saboda haka ya kamata su kusa kai ga cinma burin aiki 11 (ajanda 11) da shugabancin jihar ta shirya.

Fintiri ya kara gargadin su kan cin hanci da rashawa da almubazzaranci da dukiyar jama’a sannan ya shawarce su da su kasance masu gaskiya da adalci da ga dukkan mutane da kuma tafiyar da kowa akan tsarin mulki.

A yayin mayar da martani a madadin sababbin shugabannin da aka rantsar, shugaban karamar hukumar Michika, Micheal Shehu, ya gode wa gwamnan, PDP da jama’ar jihar da suka basu wannan damar don yin hidima.

A cewarta, za su yi aikinsu cikin gaskiya da adalci tare da tsoron Allah tare da bayar da rabon dimokiradiyya ga mutanensu, tare da tabbatar da cewa ba za su kunyatar da mutanen da suka zabe su ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babachir da APC Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Adamawa.

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), reshen Adamawa, sun yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar.

Mista Babachir Lawan, a cikin wata sanarwa ya ce ba a gudanar da zaben a karamar hukumarsa (Hong) ba.

“Duk da tabbacin da gwamnan jihar Adamawa ya bayar cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar da adalci da gaskiya, amma ba a yi zaben a cikin Hong ba, ba zabe ko a cikin mazaba daya.” inji Babachir.

Labaran Siyasa

2023: Kalli Yankin Da Matasan Arewa Suka Ba wa Goyon baya Ga Shugabancin Kasa

Published

on

Wata gamayyar kungiyoyin matasan Arewa ta yi kiran da a sauya shugabancin kasar daga arewa zuwa yankin Kudu maso Kudu kafin zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Hadin gwiwar, a karkashin kungiyar ‘Arewa Youths Assembly’, ta ce ba zai zama da adalci ba ga Arewa ta fito da shugaban Najeriya na gaba tare da lura cewa yankin ta mamaye matsayin fiye da sauran yankuna tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta a 1960.

Saboda haka, kungiyar sun bayyana cewa sun fara neman dan takara daga Kudu maso Kudu mai shekarun haifuwa tsakanin shekara 40 zuwa 50 da zai karbi shugabanci daga Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Shugaban kungiyar, Mohammed Salihu Danlam ne ya bayyana wannan matsayin kungiyar a gaban wani taron manema labarai a jiya.

Yayin da Danlam ke jawabinsa, ya bayyana cewa dan takarar “dole ne ya kasance yana da cudanya na kwarai da kasashen duniya, dole ne ya shiga cikin tsarin mulki na lokaci mai tsawo, ya kasance da kwarewar sadarwa, dole ne ya zama iya ba da fifikon tabbatar da adalci na zamantakewa da kyautatawa kan ci gaban tattalin arziki.”

“Arewa ta mamaye matsayin shugabancin kasar nan tun lokacin da ta sami ‘yancin kai, fiye da kowane yanki; lokaci ya yi da matasan Kudu maso Kudu za su fitar da shugaban kasa shekarar 2023,” in ji Danlam.

“Najeriya kasa ce da ke baya a tsakar cin gaba da alkawurai da kuma zama cikin duhun rashin adalci. Muna rayuwa da rashin tabbas. A yadda abubuwa suke a yanzu, bamu da masaniyar al’ummar da za su faru idan Arewa ta ci gaba da mulki a 2023. inji shugaban Kungiyar Matasan Arewa.

 

Continue Reading

Labaran Siyasa

Gombe: Dankwambo Ya Caji Membobin PDP Da Su ci Gaba da kasancewa Da Hadin Kai

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya tuhumi membobi na jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar Gombe da su kasance da hadin kai.

Tsohon gwamnan jihar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron PDP a Gombe ranar Litinin din nan da ta gabata.

Dankwambo wanda tsohon mataimakinsa, Charles Iliya ya wakilta a jawabin, ya bayyana da cewa ayyukan raya kasa a jihar duk a karkashin gwamnatin PDP ne.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Nuhu Poloma, yayin da yake nasa jawabi ya bayyana cewa an kayar da PDP a lokacin babban zaben shekarar 2019 ne saboda sun ki sakacci da yawa.

Poloma ya kara da cewa har yanzu jam’iyyar na da karfi sosai a jihar, duk da kayen da aka yi masu a babban zaben.

Shugaban PDP din ya gargadi mambobin jam’iyyar da bayar da tikitin neman zabe ga daidaikun mutane da suka ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar koda aka kashe su a jam’iyyar.

Shi kuma Shugaban Jam’iyyar PDP a Bauchi, Hamza Akunya, yayin da yake magana ya ce jam’iyyar ta sha kaye a babban zaben saboda ayyukan wasu membobin jam’iyyar da wasu jam’iyyu.

Akunya ya lura cewa, mambobin jam’iyyar PDP da suka fice daga jam’iyyar nan ba da jimawa ba zasu dawo.

“Shawarata a gare ku ita ce ku samar da sahihan ‘yan takara ga zaben 2023 wadanda zasu iya kayar da ‘yan adawa daga wasu jam’iyyu,” in ji shi.

Wata tsohuwar ‘yar majalisar wakilai, Binta Bello, yayin da take magana ta bayyana cewa an gudanar da taron ne domin hadin kan mambobin jam’iyyar.

Bello wadda itace ta shirya taron ta kara da cewa dole ne membobin jam’iyyar su fahimci cewa har yanzu jam’iyyar tana da karfi a jihar Gombe kuma a shirye take ta taka rawar gani

Continue Reading

Labaran Siyasa

‘Yan Najeriyar Za Su Fuskanci Mawuyacin Yanayi A Karkashin Mulkin Buhari a 2020 – Shehu Sani

Published

on

Shehu Sani, tsohon Sanata wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a jagorancin Sanatoci na 8 na Najeriya, ya ce ‘yan Najeriya za su kara fuskantar wahala a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2020.

Naija News ta samu labarin cewa tsohon dan majalisar ya yi wannan tsokaci ne yayin wani shirin rediyo a gidan Rediyon Invicta FM a Kaduna ranar Lahadin da ta gabata.

Tsohon Sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani a ranar Laraba ya yi alfahari da cewa bai janye daga siyasa ba, yana nan dawo nan da shekarar 2023.

Shehu ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Kaduna lokacin da kungiyar Magabata na Sabon Garin Nassarawa suka ba shi wata kyautar lambar yabo don kyakyawan aikinsa da kuma halin karimci ga wakilcin al’umma.

Continue Reading

Trending