Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 10 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 10 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Bar Najeriya Zuwa Kasar Masar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata, 10 ga Disamba, 2019, ya bar Najeriya zuwa Aswan, kasar Egypt, don halartar taron Aswan.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an tsara dandalin ne don kawo Cigaba ga Afirka.

2. Dalilin da yasa Ban halarci Shirin Kyautar Soyinka ba – Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya dora laifin a kan ci gaba da tsare Omoyele Sowore, mai wallafa labarai ta yanar gizo na Sahara Reporters, cewa saboda wannan ne ya sa ya ki zuwa Cibiyar Nazarin Bincike ta Wole Soyinka.

Naija News ta fahimci cewa ya kamata a karrama Osinbajo ne da lambar yabo a wannan hidimar saboda rawar da ya taka a aikin tabbatar da adalci a jihar Legas, yayin da ya kasance kwamishinan jihar da kuma Attorney General.

3. Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Shugaban FIRS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Muhammad M. Nami a matsayin sabon shugaban hukumar ‘yan rebenu ta Tarayya (FIRS).

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, an bayyana nadin Nami ne a cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Litinin bayan da Garba Shehu, Babban mai ba da shawara na musamman kan harkar yada labarai ga Shugaban kasa ya sanar da hakan.

4. Zaben Kogi: Natasha Ta Gabatar Da Karar Rashin Amince Da Zaben Bello a Kotu

‘Yar takarar kujerar gwamna a jihar Kogi a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna a ranar 16 ga Nuwamba 2019, Natasha Akpoti, ta tunkari kotun kolin zabukan gwamnoni kan sakamakon zaben.

A cikin takardarta, Barr. Akpoti ta shigar da kara a gaban kotun a ranar Asabar da daddare, na neman a soke zaben.

5. Sarautar Tinubu Ya Kare, Sowore A Yanzu Shine Sabon Shugaban Yarbawa – Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce zamanin Bola Tinubu a matsayin jagora a kasar Yarbawa ya kare saboda Omoyele Sowore, jagoran kungiyar #RevolutionNow, a yanzu shine sabon shugaban Yarbawa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, Kanu ya yi wannan bayanin ne yayin wata faifan rediyo a gidan Rediyon Biafra a ranar Lahadi, 8 ga Disamba, inda ya yi magana kan cin zarafin Sowore da jami’an DSS suka yi da kuma cin zarafin bil adama a Najeriya.

6. 2023: Arewa Ta Bada Buqatar Da Zai Sa Su Mikar da Shugabanci Ga Kudu

Wata kungiyar Matasan Arewa ta yi gargadi game da shirin yankin na mika mulki ga Kudu a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kare wa’adinsa a shekarar 2023.

Dangane da bayanin matasan da ke gudana a karkashin kungiyar Arewa Youths Consultative Forum, AYCF, sun ce cin mutuncin ‘yan Arewa da ake yi a Legas daga hannun kungiyar Task Force na sa Arewa matukar yin nazari kan mikar da kujerar shugabanci ga kudu.

7. Miliyoyin ‘Yan Najeriya Ba Su Damu Da Sake Kamun Sowore Ba – Femi Adeshina

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa miliyoyin ‘yan Najeriya ba su damu da batun sake kamun Sowore da ma’aikatar Tsaro ta sake yi ba a babbar kotun tarayya a makon da ya gabata.

Adesina ya bayyana hakan ne a shirin Tashar Talabijin ta Channels a ranar Litinin lokacin da aka nemi ya bayyana matsayin sa game da mamaye Kotu don kamo Omoyele Sowore.

8. Muna Zantawa Buhari Kan Yanayin El-Zakzaky – Gwamnatin Iran

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa tana cikin tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya kan batun jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, IMN, da aka fi sani da ‘Yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Abbas Mousavi, ya ce kasar tasu ta hanyar diflomasiya, tana hulda da gwamnatin Najeriya kan yanayin halin da El-Zakzaky ke a ciki.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a koyaushe a Naija News Hausa