Connect with us

Uncategorized

Bayani Daga Taron Sarakunan Gargajiya Na Arewa Da Ya Gudana A Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Manyan Sarakunan Gargajiya na Arewa sun gudanar da wata Babban Taronsu na 6 a jiya a Kaduna don tattaunawa kan abin da suka bayyana a matsayin kalubale da yawa da ke addabar yankin arewa, hadi da tarayyar kasar.

Shugaban kungiyar Sarakunan gargajiya na Arewa, Mai Martaba Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar, yayin da yake jawabi a wajen taron ya ce tabbatar da zaman lafiyar kasar itace babban fifiko a garesu.

Yayin da yake tabbatar da gwamnati a cewa sarakunan gargajiya abokan huldar su ne na ci gaba a kowane mataki, ya jaddada da cewa “za mu ci gaba da ba gwamnati shawara kan abin da ya kamata kuma mun yi imani cewa gwamnati za ta saurare mu.”

Ya kuma tabbatar wa gwamnati cewa cibiyar gargajiya ba ta da wata sabani da gwamnati, tare da tabbatar da cewa “wannan cibiyar tana hadin gwiwa da gwamnati kuma babban mai ruwa da tsaki ne gwamnati a kowane mataki don neman shawarwari mai kawo ci gaba.”

Ya tunatar da sarakunan gargajiyar kan bukatar bayar da gudummawarsu ta yadda za a shawo kan matsalolin da suke fuskanta, yana mai cewa “ga gwamnoninmu, za mu tallafa masu idan suna da shirye-shirye masu kyau. Za mu yi aiki tuƙuru don ganin mun sami nasarar kammala shirye-shiryen su.”

A haka kuma Gwamnan Jihar Kaduna, gwamna Nasir El-rufai, wanda mataimakinsa, Dakta Hadiza Balarabe ya wakilta, ya yi kira ga kungiyar ta gargajiya da ta ci gaba da taka rawarta a matsayinta na jagorar al’umma tare kuma da kara karfafa gwiwar matasa a cikin al’ummominsu da su bayyana manufofin gwamnati da zai inganta matsayin rayuwa da kawo ci gaba.