Connect with us

Labaran Najeriya

Karanta Korafi Da Zargin Da Aisha Buhari Ta yi wa Garba Shehu Da Mamman Daura

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta aika da sakon kalubalanta da zargi ga Mamman Daura, dan uwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da cewa yana bada umarni ba tare da yardar Shugaban kasar ba.

Naija News Hausa ta gane da cewa rashin jituwa tsakanin uwargidan shugaban kasar da dangin Mamman Daura ya bayyana ne a fili a watan Oktoba bayan da Aisha ta dawo daga tafiyarta a Turai.

An hangi Aisha Buhari a wani faifan bidiyo tana ta tambayoyi game da dalilin da yasa aka kulle dakinta, sannan kuma ta bukaci Iyalan Daura da su fita daga cikin gidan da aka gina da gilashin.

Uwargidan shugaban a cikin wata sanarwa da aka bayar wa Aminiya a safiyar Laraba ta ce Mamman Daura ya ba da umarnin cewa a rusa ofishin uwargidan shugaban kasa ta hanyar amfani da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu.

A’isha Buhari, a cikin wata sanarwa da aka yi wa lakabi da “Garba Shehu Ya Wuce Gona Da Iri”,  ta ce umarnin ya zama abin kunya ga shugaban.

Bayanin wanda uwargidan shugaban kasa ta fitar ta hanyar samar da sako a yanar gizo (email) din Suleiman Haruna, mai magana da yawun A’isha Buhari ta ce:

“Ci gaban Najeriya ya dawama ne kan jami’an gwamnati da aiwatar da ayyukansu yadda ya dace cikin fasaha da kuma zama abin misali a fannoni daban daban bisa kokarinsu. Ba alama ce mai kyau ba yayin da jami’ai suka yi watsi da abin da ya shafe su da kusa kai akan yin alamuran da bai shafesu ba.”

“A matsayin kakakin Shugaban kasa, yana da babban aiki na musanman ga kare hakin Shugaban kasa da yada dukkan ayyukan alheri da yake aiwatarwa a kasar. Maimakon fuskantar wannan nauyin da gaskiya, ya karkatar da amincinsa ga Shugaban kasa ga wasu da ba su da tushe a cikin yarjejeniyar da Shugaban kasar ya rattaba hannu tare da ‘yan Najeriya a ranar 29 ga Mayu, 2015 da 2019.”

“Don kara tabarbarewa, Mallam Shehu ya gabatar da kansa ga wadannan mutane a matsayin kayan aiki na yarda da aiwatar da manufofinsu, tun daga bangaren iko har zuwa matakin tsoma baki cikin al’amuran dangin Shugaban kasa. Wannan bai kamata ya zama haka ba. Matakin tsoma baki a cikin al’amuran Uwargidan Shugaban kasa wata ci gaba ce ta ayyukan ɓarna daga waɗanda ke aiken sa.”

“Dukkanmu mun tuna cewa Mamman Daura ya sanya wa kansa da iyalinsa wani sashe a fadar Shugaban Kasa, inda ya yi kusan shekaru 4. Da kuma lokaci ya kawo don ficewarsa, ya shirya dauki matakin kutsa kai ga sirrin iyalina ta hanyar bidiyo da aka watsa a kan yanar gizo ta hannun diyar sa Fatima Mamman Daura, an bayyana a fili ga jama’a alamun cewa lokacin da na shigo ƙasar ne Shugaban ƙasar ya kulle ni daga shiga daki na. Garba Shehu a matsayinsa na mai magana da yawun shugaban kasa ya san gaskiyar lamarin, kuma yana da alhakin shirya bayanai a kai tsaye don bada hasken yanayin ga jama’a, amma saboda biyayyansa ga wasu can daban da kuma yadda ya watsar da adalcinsa, da gangan ya ki bayyana gaskiyar lamarin a madadin Shugaban kasar da ya nada shi tun farko. Sakamakon haka, wannan ya nuna da cewa ya rushe aminci da ke tsakaninsa da Iyali na farko da ta sanya shi ga matsayi.”

“A wannan lokacin ne na tuno da abin bakin ciki cewa wannan Garba Shehu ne ya yi ikirarin cewa gwamnati ba za ta bar ofishin Uwargidan Shugaban kasa ta tsaya ba. Daga baya ne ya tabbatar wa daya daga cikin ma’aikatana cewa Mamman Daura ne ya umurce shi da ya fadi haka ba Shugaban kasa ba. Wannan tururuwa ta jawo hankalin matan Najeriya. Bai san gaskiyar cewa ofishin First Lady ta riga ta zama al’ada ga dokar kasa ba.”

Uwargidan shugaban kasa wacce ba ta gamsu da matakin na Garba Shehu ba ta ba da kakkausan gargadi ga kakakin Shugaban kasar.

Ta kara da cewa, “Garba Shehu yana bukatar fahimtar cewa ba za a kara amince da irin wannan halayyar ba”.