Connect with us

Uncategorized

‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Darakta, Firinsifal da Dalibai 3 A Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton su da matsayin ‘yan garkuwa sun sace Daraktan ma’aikatar shari’ar jihar Adamawa, Barista Samuel Yaumande, da wani Firinsifal na Makarantar Sakandiri da wasu mutane 3 a Sangare, kusa da Jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama (MAUTECH) a Yola.

A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun mamaye gidan Daraktan ne a daren Litinin din nan da ta gabata da misalin karfe 9:15 na yamma, dauke da muggan makamai suka fyauce da shi tare da makwabcin su wanda ke da matsayin firinsifal na wata makaranta tare da dalibai 3.

Majiysar ta ce sun zo ne dauke da manyan makamai da harbe-harben bindigogi a sama don tsoratar da mazauna yankin. Bayan harbe-harben bindigar da suka yi na ‘yan mintoci, ‘yan bindigar sun yi nasarar da sace daraktan, shugabar makarantar, da kuma wasu dalibai 3.

“A yanzu haka dai, ba mu ji daga gare su ba.” A fadin wata majiya ta daraktan a ranar Talata da yamma.

A lokacin da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa;

”Hukumar ta samu labarin zuwar ‘yan bindigar da sace Daraktan da wasu mutane 2, kuma tuni an tura mutanenmu don bin bayan masu satar. a ceci wadanda abin ya shafa.”