Connect with us

Uncategorized

Ma’aikatan Kamfanin Wutar Lantarki Sun Dakatar Da Yunkurin Yajin Aiki Da Aka Soma

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa (NUEE) ta dakatar da yunkurin yajin aiki da suka fara, ‘yan sa’o’i bayan da fadin kasar ta fuskanci rashin wutan Lantarki bisa mataki da ma’aikatar wutan lantarki ta kasar suka dauka.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Ma’aikatan Wutar Lantarki sun dakatar da yajin aikin ne bayan wani taro da wakilan Gwamnatin Tarayya suka yi a daren Laraba.

Wannan dandali na labarai ta yanar gizo ya fahimci cewa an sanar da dakatar da yajin aikin ne jim kadan bayan kammala wani taro da jami’an gwamnatin tarayya inda kungiyar ta amince da cewa zai dakatar da matakin yajin aiki na kwana daya da suka yi a fadin kasar.

Comrade Joe Ajaero, Shugaban NUEE na kasa, ya tabbatar da sakamakon taron ne ga manema labarai, ya kuma kara da cewa sun kammala tattaunawa da gwamnatin tarayya kuma an fahimci korafin ma’aikatan.

Ya ce an magance dukkan matsalolin kungiyar da membobinta ta gabatar a yayin ganawar wacce ta dauki lokaci har zuwa safiyar yau, Alhamis, 12 ga Disamba.

“Mun kammala tattaunawa kuma an magance dukkan matsalolin amma muna jiran aiwatarwa. Amma duk da hakan mun dakatar da yajin aikin.” Inji shugaban kungiyar ta NUEE.

Naija News ta bayar da rahoton cewa kungiyar ta shiga yajin aikin ne bayan damar kwanaki 21 da kungiyar ta NUEE ta gabatar ga Minista Wutan Lantarke, Saleh Mamman, don aiwatar da bukatunsu da gazawar ministan don tattaunawa da kungiyar cikin kwanakin da suka yanka wa hukumar wacce ta karshe a daren Talata.

Sakamakon yajin aikin wanda ya fara a safiyar ranar Laraba, Najeriya ta sami rashin wuta a fadin kasar baki daya. Matakin yajin aikin ya haifar da rufe mafi yawan ofisoshin Kamfanin rabas da wutan Lantarki (Discos) a fadin kasar.