Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: Mutane 28 Duk ‘Yan Gida Guda Sun Mutu A Hadarin Mota A Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kimanin mutane 28 da aka bayyana a matsayin dangi daya ne aka ba da rahoton cewa sun kone kurmus fiye da gane wa a ya yi wata sabuwar hadarin wani mota da ya afku a kan babbar hanyar Ningi da ke jihar Bauchi.

Naija News Hausa ta fahimta bisa rahoton da jaridar PUNCH ta bayar da cewa hadarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis (yau).

Da wakilin labaran Punch ya zanta a wata tattaunawa ta wayar tarho da wani dangin wadanda abin ya shafa, Abdullahi Yamadi, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bayyana shi a matsayin “abin bakin ciki.”

Yamadi, wanda aka bayyana shi a matsayin Sakatare na Kungiyar Manema Labarai na Yankin Arewa-maso-Yamma ta Najeriya, ya ce wadanda suka mutu dukkansu danginsa ne.

Ya ce suna kan hanyarsu ne zuwa Yola, jihar Adamawa a lokacin da lamarin ya faru da su.

“Ee, hatsarin gaskiya ne kuma duka wadanda suka mutu ‘yan uwana ne. Duk Suna kan tafiya ne zuwa Yola, jihar Adamawa, don ziyara a lokacin da lamarin ya faru” inji bayanin Yamadi da Punch.

“Kun sani, bayan girbi da kuma a lokutan yanayi kamar haka, mutane kan yi rangadin ziyartar ‘yan uwa da suke ƙauna a wurare daban-daban; wannan kuwa shi ne sanadin tafiyar su.”

“Sun bar Dutsinma, jihar Katsina, kuma sun riga sun fice jihar Jigawa, suna a cikin yankin jihar Bauchi ne lokacin da motar su ta yi karo da wata mota. Su 29 ne a cikin motar kuma dukkansu sun mutu banda direban, wanda ya tsira.”

“Wannan mummunan labari ne kuma abin bakin ciki ne ga mutane 28 daga dangi guda su mutu a hadari guda a cikin rana guda. Abin da bakin ciki a gaskiya.”

Har yanzu a lokacin da aka bayar da wannan rahoton dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ba ta ba da sanarwar kan lamarin ba tukunna.

Idan akwai karin bayani zamu sanar a wannan shafin jim kadan.