Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari: Wani Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Yayi Magana Kan Shugaban Najeriya A 2023

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Jim Nwobodo ya bayyana cewa bai dace ‘yan siyasa su fara fada kan yankin da ta dace da shugabancin Najeriya a shekarar 2023 tun yanzu.

Nwobodo, wanda ya mallaki kujerar gwamnan jihar Anambra a lokacin jamhuriya ta biyu, ya bukaci ‘yan siyasa da su kyale Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da hankali kan mulkin kasar a yanzu.

Wannan itace bayanin tsohon gwamnan a birnin tarayya, Abuja, ranar Talata yayin gabatar da kuma kadamar da wasu littattafai guda biyu masu taken “Masanin kimiyya a majalisa da kuma mafarkin Najeriya” wanda wani tsohon dan majalisar wakilai, Dr. Eddie Mbadiwe ya rubuta.

Dan siyasar ya lura cewa mutane ne za su yanke hukunci yanki da zai fitar da shugaban ƙasa nan gaba.

“Wannan gwamnatin ba ta dade da fara wata wa’adin aiki ba. Har yau bata ma kai shekara ɗaya ba kuma muna maganar zaben 2023. Ku yi wa Allah addu’a cewa wannan mutumin yaci nasara. Ba kawai ku fara yin faɗa a kan abin da ba ku da iko ku yanke hukunci akai. Mutane za su yanke shawara idan lokacin ya yi.” inji Nwobodo.

“Zance ta taso da hanzari. Wasu daga cikin waɗannan abubuwan ba su da mahimmanci, bai dace ku fara yaƙi ba akan abin da baku da tabbacin yadda zata kasance.”

“Wasu daga cikin mutanen da suka zo nan abokan karatu na ne a jami’ar Ibadan. Nayi takara a Ibadan kuma nayi nasara a matsayin Najeriya daya. Shin har yanzu muna zaman Najeriya daya? Ina tambayar ku ‘yan jaridu. Mun rarrabu sosai.”

“Ku yi imani da ni, ina kuka saboda wannan kasar, hakika nayi kuka sosai kuma na san abin da nake fada. Wannan ba ƙasar da muka yi yaƙi akanta ba ce, mun wahala dominku kuma kuna da rawar da zaku taka a matsayin manema labarai don magana kan haɗin kai a ƙasar nan, kan adalci ga kowa.” Inji shi a karin bayani da yayi ga manema labarai.

KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Darakta, Firinsifal da Dalibai 3 A Jihar Adamawa