Connect with us

Labaran Najeriya

Babu Wata Zancen Kan Gado Da Nike Samun Yi Da Buhari – Aisha Buhari

Published

on

at

advertisement

Uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bude baki kan dalilin da yasa ta kasa yin shiru ga yin magana game da abubuwa marasa kyau da ke afkuwa a gwamnatin mijinta.

Ta bayyana cewa ba ta da tattaunawa mai zurfi a kan gado tare da mijinta saboda karancin lokaci da suke da ita.
“Wannan itace dalilin da yasa na kasa yin shiru da magana” inji Aisha.

A yayin zantawa a wata shirin manema labarai na Talabijin a tarayyar Kasa (TVC), uwargidan shugaban ta ce hakan ta kasance ne saboda sun shagala da lamuran kasar.

Ana tambayar Aisha, wacce a koda yaushe take ba da ra’ayinta game da batutuwan da suka shafi kasa, an tambayeta wata kila ko ta gabatar da wasu daga cikin waɗannan batutuwan ga shugaban ƙasa, mijinta yayin “kwancin su a gado dadare”.

Sai kuwa ta amsa da murmushi. “Babu wata zance da muke a kan gado”.

An kuma tambaye ta “ba ma ko a cikin wancan dakin ba”, watau ana nufin ne kalaman mijinta a cikin shekarar 2016 mai cewa “Matata ta kasance ne a bangaren kicin da falo na, da kuma wancan dakin” fadin shugaba Buhari.
Ta sake cewa, “a’a”.

A cewarta, tsarin tafiyarda ayukan kasar ya hana su irin wannan mahamala sabili da karancin lokaci.
Ta na mai cewa idan membobin majalisar zasu aiwatar da ayyukansu kamar yadda ya dace, to da ita da mijinta za su iya samu lokacin hutawa, kuma idan hakan ya faru, ba lallai ne ta ci gaba da tofa albarkacin bakinta ba a lamuran da ke afkuwa ba.

“Babu wata lokacin zancen kan gado a cikin Villa. A’a babu, saboda da yawancin lokatai mukan shagala ne da sauraron labari kowace iri a kowace lokaci. Ina zaton da dubin cewa da mutanen da ya sa a cikin majalisar aikinsa, da zai dace su zauna su yi nazari da kuma aiwatar da ayukan da ya dace da abin zai fi kyau. Wannan shine dalilin da ya sa ba shi da kyau a kasance da wani mai fadi aji can boye,” in ji Aisha.

“Dole ne kawai mu zabi mutanen da suka dace da za su kasance a matsayin da ya dace domin mu huta, domin kuma matar shugaban kasar ta daina maganganu.”