Uncategorized
Karanta Dalilin Da Ya Sa Wani Mutumin Ya Kashe Dansa
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wani mutum dan shekaru 40 da haihuwa da ake kira Musbahu, bisa zargin kashe dansa mai shekara uku.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin kamfanin dilancin labarai ta DAILY POST a ranar Juma’a.
Ya yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Mahaukaci Quarter, a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano.
Haruna ya ce mutumin wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan an karshe bincike akan lamarin.
Da yake magana da manema labaran DAILY POST, Musbahu, wanda riga ya amsa da amince da laifin da ake zarginsa da ita ya ce, ya aikata laifin ne domin ya ceci dansa da kan shi daga abin kunya, da cewa yaron an haife shi ne tun basu yi aure ba kuma ba shi da wanda zai taimaka masa da kula da yaron.