Connect with us

Labaran Nishadi

Kalli Jerin Kwararrun ‘Yan Fim Na Hausa Da Muke Da Tarihin Rayuwarsu A Rubuce

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa a sashen mu ta Nishadi mun ruwaito da Tarihi da Takaitaccen Labarin ‘yan shirin fim a Kannywood da dama cikin ‘yan watanni da suke shige.

Na farko a jerin tarihin ‘yan kannywood da Naija News Hausa ke dauke da shi itace Fati Washa, ba son kai ko wata ban girma ba amma itace na farko da kuma wacce aka fi neman karanta tarihinta a shafin mu.

Karanta Jerin suna da Adadin labaran rayuwarsu a kasa;

1. Fati Washa

Fatima Abdullahi Washa sananiyar akta ce a Kannywood. Sunar ta a filin wasa itace Fati Washa.  an haife ta ne a Watan Biyu 21, 1993, a Jihar Bauchi. a santa da sunaye kuma kamar haka; Tara Washa ko kuma Washa. A shekara ta 2018, Fati Washa na da shekaru 25. Kuma bata da Aure. Kyakyawa ce kuma da hasken jiki, Fati Washa tana daya cikin masu tsarin fim wanda ake fahariyya da su a Kannywood.

Akwai sani da cewa ita Kyakyawar yarinya ce kuma daya daga cikin yan wasan fim dake da tsadar kamu a Kannywood. Da yawa a cikin masoyan ta kan so ta a nishadi da kuma neman ta a facebook da sauran fillin nishadi don darajata ta ga aikin ta. Ci gaba da karanta labarin Fati Washa.

2. Ali Muhammad Idris (Ali Art Work)

Dan matashin mai suna Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Ali Artwork, an haife shi ne kuma ya girma ne Jihar Kano, a Yankin Tarauni ta Jihar Kano.

Kamar yadda na san kuna muradi na so gane ko shi dan shekara nawa ne

An haife Ali Muhammad Idris ne a ranar 1 ga Watan Janairu, a shekara ta 1992.
Ya fara makarantar firamare ne a wata Makaranta mai Suna Unguwan Uku Firamare Sukul a shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2005. ya karasa da karatun sa a Makarantar sakandare farko watau (JSS 1) a Wata Makarantar sakandare ta gwamnati daga shekara ta 2005 zuwa 2008,  bayan kammala wannan ya samu dace da ci gaba da karatun sakandaren a wata sakandare na Kundila, watau GSS Kundila daga Shekara ta 2008 zuwa 2011. Ci gaba da karanta labarin Ali Art Work.

3. Ummi Ibrahim – Zee Zee

An haifi Ummi ne a Jihar Borno a shekara ta 1989. Tsohon ta Ba’Fullace ne, uwar kuwa ‘yar Arab ce.

Ummi ta bayyana shahararun ‘yan wasa da ta ke ji d su da kuma take koyi da su sosai wajen shiri.

“Wadanda na ke ji da su kuma na ke koyi da su a filin wasan Kannywood sune kamar haka; Marigayi’a Aisha Dan-Kano da Marigayi Rabilu Musa Dan-Ibro. muna ba wa juna girma sosai da gaske, Allah ya gafarta masu” in ji ta a wata ganawa da ta yi da manema labaran (Information Nigeria) shekara da ta gabata. Ci gaba da karanta labarin Zee Zee.

4. Sani Danja

Sani Danja, kamar yadda aka fi sanin sa da suna, daya ne daga cikin shaharrarun ‘yan shirin fim ba Kannywood da ake ji da su.

Ainihin sunansa Danja ita ce; Sani Musa Abdullahi, ko kuma Sani Musa Danja.

An haifi Sani Danja ne a ranar 20 ga watan Afrilu ta shekarar 1973 a nan garin Fagge, ta Jihar Kano, a kasar Najeriya. Bincike ya bayyana da cewa Sani Musa Abdullahi ya samu likin Danja ne a lokacin da yake karami, dalilin suna kuwa itace irin halin da Sani ke da shi na rashin ji a lokacin. Kawai abokanan wasa suka laka masa sunan ‘Danja’ wanda a yau ko ina ka kira Sani Danja an riga an gane ko da wa kake. Ci gaba da karanta labarin Sani Danja

5. Rahama Sadau

An haifi Rahama Ibrahim Sadau ne a ranar 7 ga watan Disamba, a shekarar 1993 kamar yadda ‘Wikipedia’ ta bayar. Ta kuma yi zaman rayuwarta ne da iyayen a Jihar Kaduna tun daga haifuwa.

Rahama Sadau tayi karatun jami’a na farko ne a Makarantan Fasaha ta Jihar Kaduna da aka fi sani da (Kaduna Polytechnic), inda ta karanta ‘Business Administration’ a matsayin kwas na ta.

Sadau, ta kara da karatun ta na karanta kwas din ‘Human Resource Management‘ a wata babban Makarantar Jami’ar Eastern Mediterranean University in Northern Cyprus a shashin bincike akan sana’a da tattalin arziki. Ci gaba da karanta labarin Rahama Sadau.

6. Maryam Booth

Maryam Ado Muhammed, wata Kyakyawa da aka fi sani da Maryam Booth, Shahararra ce a fagen wasan kwaikwayo na Kannywood, Tana kuma da Fasaha wajen aikin Dinke-dinke.

Maryam Ado Muhammed ‘yar haifuwar Jihar Kano ce a arewacin Najeriya, an kuma haife ta ne a ranar 28 ga Watan Oktoba, a shekaran 1993.

Mahaifiyarta Maryam kuwa Ita ce, Zainab Booth, Ita ma kwararra ce kuma daya daga cikin wadanda suka dade a shirin wasan kwaikwayo na Kannywood. Haka Kazalika dan uwan Maryam, watau Ahmed Booth, shi ma Gwarzo ne a filin hadin Fim na Kannywood.

Ko da shike Kaka ta Mace ga Maryam Fulani ce, amma Kakanta namiji dan Turai ne, daga Scotland. Ci gaba da karatun labarin Maryam Booth.

7. Umar M. Sharif

Umar Muhammadu Sharif yana daya daga cikin Shahararrun mawaƙan hausa masu mahimmancin kwarari da gaske.

Sharif ba Mawaki ne kawai ba, Dan kasuwanci a fagen wasa, yana kuma da kyautannai lambar yabo mai yawa da ya karba a fagen shiri.

An haifi Sharif ne a shekarar 1987, ya kuma yi karatun Makarantar Firamare da Sakandiri ne a garin su, Rigasa ta Jihar Kaduna.

Umar ya bayyana da cewa shi ya kasance ne dalibi mai mahimmanci kuma tun lokacin yarantakarsa, abin da ya sa shi cikin raira waƙa shi ne wani abin da ya faru tsakanin shi da ƙaunarsa na farko, kamar yadda ya fada wa BBCHausa. Ci gaba da karatun labarin Umar M. Sharif.

8. Ali Jita

Ali Jita shahararran mawaki ne mai zamaninsa a Kano, sananne ne kuwa a wake-wake a fagen shirin finafinan Hausa, kuma ya shahara kwarai da gaske a yawancin finafinan hausa.

Ainihin sunan sa itace Ali Isa Jibril, kuma an haife shi ne a unguwar gyadi-gyadi a cikin badalar Kano dake a Arewacin Najeriya.

Ali yayi karatun farkon sa na Firamare ne a wata makarantar da Sakandare duk a birnin Legas, a wata makarantar sojojia, kamin dada ya bar Legas zuwa brinin Tarayyar kasa, Abuja. Ci gaba da karanta labarin Ali Jita.

9. Bilikisu Shema

Kyakkyawa da kuma shahararriyar, Bilkisu asalinta ‘yar Jihar Katsina ce. An haifi Bilikisu Shema ne a ranar 28 ga Watan Yuli a shekarar 1994.

Fitacciyar, Shema ta fara karatun ta na firamari ne a makarantar Isa Kaita College of Education, bayan nan ta shiga sekandari a Government Day Secondary School Dutsin-Ma.

Naija News Hausa ta gaza da samun tabbacin karatun babban jami’ar jarumar a wannan lokaci, idan hakan ya samu, zasu sami karin bayani.

Shema dai a cikin tashe a fagen fim a wannan lokaci, ita ce matashiyar jaruma wadda tauraronta yake haskawa. Ci gaba da karanta labarin Bilikisu Shema.

10. Jamila Nagudu

A takaice dai, Jaruma Jamila Nagudu ‘yar wasan finafinan Hausa ce wacce aka Haifeta a ranar 10 ga watan Agusta.

Jamila Umar Nagudu a nata bangaren Sarauniyar Kannywood ce, ma’ana, ita babbar jaruma mace ne a fagen shirya fina-finan Hausa, watau Kannywod wacce take da hedkwatarta a Kano, arewacin Najeriya.

Jarumar ta shiga fagen masana’antar fim na Hausa ne shekaru da yawa baya, amma ‘yan shekaru da suka gabata, babban Froduza na fina-finai, Aminu Saira ya sanyata a cikin fitaccen fim din da aka yi wa take ‘Jamila da Jamilu’, watau tun a fim dinne tauraron jaruma Jamila ya haska da bayyana ta ko ta ina saboda irin kwarewa da taka rawar gani a fim din. Ci gaba da karanta labarin Jamila Nagudu.

11. Nafisat Abdullahi

Nafisat Abdulrahman Abdullahi, wadda akafi sani da Nafisat Abdullahi, kyakyawa ce da kuma shahararrar ‘yar shirin fim a Kannywood, watau kamfanin hadin fim na Hausa a Najeriya.

An haifi Nafisat ne a ranar 23 ga watan Janairu ta shekarar 1991 a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Nafisat ita ce ‘ya ta hudu ga Mallam Abdulrahman Abdullahi, wani dillalin motoci da kuma dattijo masu ruwa da tsaki a kasar.
Naija News Hausa ta fahimci cewa kyakyawar tayi karatun ta na farko ne a Makarantar ‘Air Force Private School’ a nan Jos, bayan nan ta koma Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, inda ta shiga makarantar Sakandare ta Gwamnati, Dutse, Abuja. Ci gaba da karanta labarin Nafisat Abdullahi.

Ka lasa shafin Nishadi a Naija News Hausa a koyaushe don samun labaran ‘yan shirin fim na Hausa da kuma manyan labaran Nishadi ta kowace rana.