Uncategorized
Oshiomhole Yayi Watsi Da Umarnin IGP, Ya Dage A Kan Cewa Dole Ne APC Tayi Rali A Edo
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na tarayya, Adams Oshiomhole, ya dage kan ci gaba da zagayen Rali da suka shirya yi a jihar Edo.
Naija News ta tattaro cewa manyan membobin jam’iyyar APC daga Abuja sun shirya da halartar taron gangamin don marabtan tsohon dan takarar gwamna Fasto Osagie Ize-Iyamu da daruruwan magoya bayansa, daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a tasu jam’iyyar.
Kodashike, Mataimakin gwamnan jihar, Philip Shuaibu ya wallafa wata wasika ga Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, da neman ya dakatar da zanga-zangar saboda hakan na iya haifar da tashin hankali a yankin.
A yayin mayar da martani ga sakon, IGP ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Edo don tabbatar da cewa an dakatar da zanga-zangar. Amma shi Oshiomhole ya bukaci magoya bayan sa da kada su karaya, ya kara da cewa zai nemo mataki na gaba kan zanga-zangar.
“Na san cewa kun damu da gaske game da abin da muke fuskanta a nan, amma ina so in rokeku da kada ku fusata. Duk wani shugaban jam’iyya mai hankali zai yi murna da marabtan mutane daga wata jam’iyyar zuwa jam’iyyarsa,” inji shi Oshiomhole.
“Musamman lokacin da ya zama cewa masu shigo jam’iyyar sun kasance ne mutanen da suka yi gwagwarmaya da gaba da jam’iyyar a babban zaben da ya gabata inda muka fiye su da yawar kuri’u kamar dubu 50,000. Don haka muke a Benin don marabtan su amma zaka ga yadda azzaluman su ke jefa mutane cikin rikici.”
“Amma ina so in shaida muku, APC gidan mu ne ba za mu lalata shi ba kuma ba za mu bar kowa ya rusa shi ba. Ba ma son a kashe kowa, don Allah kar ku yaƙi kowa. Wadanda suka san ni sun san ni ba matsoraci bane, bana tsoron fada. Amma ba zan yi hakan ba kuma ina roƙonku da ku natsu.”
“Muna samun rahoton da ruduwa a yanzu, IG na ‘yan sanda a da ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya ba mu kariya daga taronmu. Amma a yanzu ana gaya mana cewa wannan kariyar an soke ta. Amma zan yi kira don gano menene matsalar idan ‘yan sanda suna cewa ba za su iya yi mana kariya ba ga zanga-zangar siyasa. Zan bincika kuma in sanar da ku. Amma ko da sun ce ba za mu iya bamu kariya ba, don Allah kar a yaƙi kowa. Zan haɗu da su, in nemo lokacin da za a ci gaba da zanga zangar. Amma dai zanga-zangar zata ci gaba dole wata rana… Babu wanda zai girgiza zuciyar mu. Zamu karbi ‘yan uwanmu a cikin jam’iyyar don karfafa jam’iyyar.”