Connect with us

Labaran Najeriya

Boko Haram: Leah Sharibu Ta Saura Da Rai – Bisa Bayanin Malamin Jami’a Da Aka Sace

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani Malamin Jami’ar wata kwaleji da wasu mutane goma wadanda kwanan nan ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace su, sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da su daukin matakin ceton su daga hannun ‘yan ta’addan.

Wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan kisan wasu ma’aikatan agaji hudu da kungiyar Boko Haram ta yi. ‘Yan ta’addan sun sace ma’aikatan agajin ne da a baya aka kashe a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Bitrus Bwala, wanda ya bayyana kansa a matsayin babban malami a Kwalejin Ilimi ta Gashua, a cikin jihar Yobe, a cikin wani faifan bidiyo da Ahmed Salkida, dan jaridar da aka sani da samun damar samun liki da kungiyar Boko Haram, ya bayyana cewa ya shaida da  kisan ma’aikatan hudu da ‘yan kungiyar suka yi kwanan nan a Borno.

A cikin bidiyon da aka saki, an gano wata macce wacce fuskarta ke a rufe, ko da shike ba a bayyana ko lallai Leah Sharibu ce ba.

Amma a cikin bayanin Malamin jami’ar, ya ce; “Mun lura da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya bata kokarta ba sosai kamar yadda ya kamata, shi yasa har yanzu Leah Sharibu ta saura a kame a hannun ‘yan ta’ddan Boko Haram.”

Kalli Bidiyon a kasa;

Bwala a cikin rokon sa ya bukaci kungiyar CAN ta sa baki a lamarin, ya bayyana cewa ba su cikin kwanciyar hankali a wajen saboda wadanda aka sace dukansu mabiya addinin kirista ne.

“Ina kan hanyata zuwa ofishina a ranar 27 ga Nuwamba 2019 lokacin da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka sace ni, ina kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka mana.” inji Bwala.

“Tabbas a gaban mu a kwanan nan ne aka kashe ma’aikata hudun. Kamar yadda kuke gani zaune a bayana, dukansu ‘yan uwana Kiristoci ne da aka sace a wurare daban-daban aka kawo su wannan wuri. ”

“Ina kuma kira ga Kungiyar Kiristocin Najeriya da su yi duk abin da za su iya yi a cikin karfi da damar su don su zo su cece mu; saboda lokacin da muka zo nan, mun ga wasu ma’aikata a nan, musamman ma’aikatan kungiyar ‘yan samar da abinci amma daga baya an kashe su.”

“Saboda haka muke kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi duk abin da ya dace don ganin an ceto mu. Muna kuma rokon gwamnoninmu da su zo su taimakemu su tseratar da mu.”

“Jagoran kungiyoyin Kirista a baki daya muna kira gareku da ku tattauna da gwamnatin tarayya, don ceto dukkan wadanda aka kamatan a nan.”