Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 16 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 16 ga Watan Disamba, 2019
1. Shugaba Buhari Ya Taya Ajimobi Murnan Cika Shekara 70
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi murnar cika shekara 70 da haihuwa yau, 16 ga Disamba, 2019.
Buhari a cikin wata sanarwa da ya bayar ta hannun mashawarcinsa ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya taya Abiola Ajimobi ga dimbin nasarorin da ya samu a bangarorin kamfanoni da na gwamnati.
2. Tsohon Shugaban Najeriya, IBB bai Mutu ba
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Ibrahim Badamosi Babangida (IBB), tsohon Shugaban Najeriya bai mutu ba, kamar yadda ake yada wa.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa rahotanni sun bayyana a wasu sassan kafafen yada labarai na Najeriya a safiyar ranar Lahadi, inda suke nuni da cewa Tsohon Shugaban na Najeriya ya mutu amma mai magana da yawun sa ya fitar da sanarwa inda ya karyata rahoton.
Mai magana da yawun IBB, Kassim Afegbua a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin, 15 ga Disamba, ya bayyana rahotannin mutuwar IBB da cewa “labarai ne na karya”.
3. Sharia: CAN Ta Yi Kukan Cewa A Tsige Babban Alkalin Najeriya CJN Tanko
Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi Allah wadai da kiran da babban mai shari’a na Najeriya (CJN), Muhammad Tanko ya yi, na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima don “karbar tallafawa wasu damuwar musulmai da kuma kafa dokar Shari’a.”
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Tanko Muhammad ya gabatar da wannan kudurin ne yayin da yake ayyanar taron Taro na Shekaru 20 da aka bude a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya a ranar Laraba da ta wuce.
4. APC/PDP: Dan Takaran Shugaban Kasa Atiku Ya Hade Da Asiwaju Tinubu A Jihar Neja
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a ranar Asabar da ta gabata ya gana da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.
Naija News ta fahimci cewa Tinubu ya hade da Atiku a Minna, babban birnin jihar Neja ne don karbar lambar girmamawa ta jami’ar Ibrahim Badamosi Babangida, Lapai.
Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Tinubu da mukarraban sa a lokacin da suka isa wajen hidimar.
5. Mashahurin Sarkin Kudu Maso Yamma ya Saki Matarsa ‘Yar Jamaica
Oba Abdulrasheed Akanbi, Oluwo na Iwoland, ya rabu da matar sa ‘yar kasar Jamaica, Chanel Chin.
Hakan ya bayyana ne ta bakin Sakataren yada labarai na Oluwo, Ali Ibrahim a wata sanarwar da ya bayar a ranar Lahadi.
6. Rikicin APC: Obaseki Da Shuaibu Na Barazanar Murkushe Ni – Oshiomhole
Shugaban Hidimar Zabe ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole, ya zargi gwamna Godwin Obaseki da mataimakin sa, Phillip Shuaibu da yin barazanar murkushe shi.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ta hannun Babban Sakataren yada labaran sa, Simon Egbuebulem, tsohon gwamnan jihar Edo ya ce gwamna Obaseki da mataimakinsa ba su da tasirin siyasa a yankinsu domin cin zabe.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya Ta Yau a Naija News Hausa