Connect with us

Labaran Najeriya

Ba Zani Taimakawa Kowa Ba Ga Cin Zaben 2023

Published

on

at

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya cika shekara 77 a yau Talata, 17 ga watan Disamba 2019, ya ba da sanarwar cewa ba zai fifita ko taimaka wa duk wani dan jam’iyar APC ba da ke shirin takara a zaben shekarar 2023 ba.

A cikin wata sanarwa, Shugaba Buhari, ya yi alkawarin gabatar wa ‘yan Najeriyar da zabe mai gaskiya da fifikon rikon amana.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, da wasu ma’aikatansa da mataimakan sa, wadanda suka je fadar shugaban kasar don gabatar masa da katin sakon murna da ranar haihuwa da taya shi murnar cikar sa ranar haihuwarsa karo na 77.

Buhari ya bayyana cewa duk wani dan siyasa wanda ke da niyyar tsayawa takara a zaben 2023 yakamata su fara aiki tukuru domin samun aminta daga mutanen sa.

Ya kuma kara da cewa ba zai tallafa wa kowa ba ko dauka matakan tauye ra’ayin ‘yan Najeriya a zabe na gaba ba a kasar.

Shugaban ya jaddada wa membobin jam’iyyarsa cewa “duk wanda ke son tsayawa takara dole ya yi aiki tukuru domin ba zai amince da kowa ba da amfani da matsayi ofishin sa ba domin neman goyon baya zaben.”