Connect with us

Uncategorized

APC Tayi Rashi A Yayin Da Wani Sanata Ya Mutu A Jihar Imo

Published

on

at

Sanata Benjamin Uwajumogu, Sanata mai wakiltar mazabar Arewacin Imo a majalisar dattijan Najeriya ya rasu.

Naija News ta rahoto cewa Sanata Uwajumogu ya fadi ne cikin makewayin gidansa a yayin da yake wanka, an garzaya da shi wani asibiti mai zaman kanta a Apo, cikin Abuja, babban birnin Najeriya, inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

Wannan dandali na labarai ta yanar gizo ta fahimci cewa Sanata Rochas Okorocha, wanda ke wakiltar mazabar Imo West Senatorial, ya tabbatar da mutuwar Uwajumogu ga manema labarai a Majalisar Dattawa a ranar Laraba, 18 ga Disamba.

Mun samu labarin cewa an fara jinyar Sanata Uwajumogu ne a Hadaddiyar Daular Larabawa, Saudiyya saboda doguwar rashin lafiya da yake dauke da shi, amma a kwanan nan ya dawo Abuja bayan ya nuna alamun murmurewa, a cewar wata majiya da ta san halin da yake ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ya ba da rahoton cewa har zuwa mutuwarsa, Sanata Uwajumogu ya kasance memba ne a jam’iyyar All Progressives Congress, jam’iyyar da ke mulkin Najeriya.