Connect with us

Uncategorized

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Sanar Da Shirinta Na Gina Masallacin Juma’a 90

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da shirinta na gina masallacin Juma’a 90 inda al’umma zasu rika yin salla biyar na kowace rana.

Hakan ya bayyana ne daga bakin kakakin ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Isma’il Ibrahim, wanda ya tabbatar da wannan ci gaba kuma ya kara bayyana cewa sama da ‘yan kwangila 200 ne suke neman a yardar masu da yin aikin gina masallatan wadda za a gina a gundumomi 30 na jihar.

Ya kuma bayyana cewa Ghali Mu’azu wanda shi ne wakilin Hukumar Kula da Yanayin Kasa da Ofishin Kula da Ayyuka, ya ce tsarin zabar yan kwangilar zai zama a bude, da adalci da kuma gaskiya.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babbar kotun jihar Kano ta baiwa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ganduje ikon cire duk wani sarki a cikin a bisa tsarin doka.

Mai shari’a A. T. Badamasi wanda ya sanar da haka a yau a Kotu bayan ya ki bayar da damar tsawaita karar umarnin  hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar kutsa kai da kuma iko kan masarautar Kano.