Connect with us

Uncategorized

Kotu Ta Yanke Hukuncin Tabbatar Da Zaben Gwamnan Nasarawa, Gwamna Sule

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun koli, a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba 2019 ta amince da zaben Abdullahi Sule a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Kwamitin mutane bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Mary Peter-Odili ta yi watsi da karar da David Ombugadu da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka yi kan nasarar Sule a zaben da aka yi ranar 9 ga Maris, 2019.

Mai shari’a Peter-Odili ya ce karar da Ombugadu ya yi bashi da wata daraja da muhinmaci.

Ku tuna cewa Jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamna na 2019, Mista David Ombugadu a watan Agusta sun nemi Kotun daukaka kara a Nasarawa domin ba da umarnin a sake sabon zabe a jihar.

Lauyan jam’iyyar PDP, Mista Wale Olanikpekun, SAN, yayin da ya ke bada jawabinsa na karshe kan karar, ya yi zargin cewa INEC bata cika ka’idojin tantancewa ba sama da kashi 90 cikin 100 na sassan zabe a jihar.

Ya ce sun bayar da ingantattun korafe-korafen masu kada kuri’a ga kotun, ya kara da cewa, “yawan kuri’un da suka mayar da gwamnan bai yi daidai da yawan masu kada kuri’a da ke cikin takardan rajista ba”