Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 18 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 18 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugaba Buhari ya Sanya Hannu a kan Kasafin Kudi na shekarar 2020

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 17 ga watan Disamba 2019, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 a cikin doka.

Naija News ta samu fahimtar cewa shugaban ya yi rattaba hannu ne ga kasafin kudi Naira miliyan 10.5 a ofishin fadar Shugaban kasa, Abuja.

2. Kotu ta yi kira ga Malami da Daraktan DSS bisa tsare Sowore

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta nemi halartar Ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami, SAN, da Darakta-Janar na ma’aikatar Gwamnatin DSS, Yusuf Bichi, a kan ci gaba da tsare jagoran zanga zangar neman juyin mulki, Omoyele Sowore.

Kotun, a hukuncin da aka yanke ta wanda Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar, ta ba da umarnin cewa mutanen biyun da su bayyana dalilin da ya sa ba zasu sake sakin Sowore din ba daga akwaman su.

3. Orji Kalu ya Nemi Beli bayan Hukuncin Yin Shekaru 10 a Jaru Da Aka Yanka Masa

Sanata mai wakiltar mazabar Abia-North Senatorial, Orji Uzor Kalu, wanda aka samu da laifin zamba na kudi kimanin biliyan #7.6bn tare da yanke masa hukuncin shekaru 12 a kurkuku, ya roki kotun da ta bayar da belin sa.

Tsohon gwamnan jihar Abia din a cikin wata takardar neman beli da ya gabatar a gaban kotu ranar Talata ya ce yana fama da kalubalen lafiyar jiki wanda likitocin gidan yarin ba za su iya kula da shi ba.

4. Yadda El-Rufai Ya Nuna Mini Nasarar Buhari Tun Kafin Ma Zabe Ta Gabato – Femi Adesina

Femi Adesina, mai ba da shawara na musamman kan kafafen yada labarai ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana tattaunawar da ya yi da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, gabanin babban zaben Najeriya.

Ya yi wannan wahayin ne a wata kasida mai taken ‘PMB a shekara ta 77:’ Don Allah ku fada wa Baba muna tare da shi har abada’, a yayin bikin tuna ranar haihuwar shugaban a ranar 17 ga Disamba.

5. Babbar Kotun Jihar Kano Ta Baiwa Ganduje Iko Kan Masarautar Jihar

Babbar kotun jihar Kano ta amince da baiwa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ganduje ikon cire duk wani sarki a cikin a bisa tsarin doka.

Mai shari’a A. T. Badamasi wanda ya sanar da haka a yau a Kotu bayan ya ki bayar da damar tsawaita karar umarnin hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar kutsa kai da kuma iko kan masarautar Kano.

6. Ba Zani Taimakawa Kowa Ba Ga Cin Zaben 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya cika shekara 77 a yau Talata, 17 ga watan Disamba 2019, ya ba da sanarwar cewa ba zai fifita ko taimaka wa duk wani dan jam’iyar APC ba da ke shirin takara a zaben shekarar 2023 ba.

A cikin wata sanarwa, Shugaba Buhari, ya yi alkawarin gabatar wa ‘yan Najeriyar da zabe mai gaskiya da fifikon rikon amana.

Ku samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a shafin Naija News Hausa