Uncategorized
Mataimakin Gwamna Kebbi Yasa ‘Yan Ta’adda Dukar Wasu Mawaka 8 Don Sukar Gwamna Bagudu
Naija News Hausa ta ci karo da hotunan wasu matasa da aka ci mutuncin su a Jihar Kebbi
Bisa rahoton da aka bayar a bayar a wasu labarai, an bayyana da cewa an yi wa matasa takwas dukansu mawaka mumunar bugu a cikin jihar Kebbi, sakamakon umarnin da Mataimakin gwamna Bagudu, Faruku Musa Yaro ya bayar ga wasu ‘yan ta’adda da su hari mawakan.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Kabiru Arzila, Musa Alle, Ayuba Ibrahim, Shamsu Attahiru, Bello kasarre, Otono da sauransu.
A cewar rahoton da Sahara Reporters suka bayar, mawaƙan an ce sun haifar da fushin mataimakin gwamnan ne bayan sun yi amfani da kalaman batanci a waƙoƙinsu don zagi da kalubalantar gwamna Bagudu.
Daya daga cikin mawakan, Arzila, ya ba da rahoton cewa an dauke su a Otal din Abacha da misalin karfe 3:30 na safiyar Litinin din nan a yayin da wasu ‘yan ta’adda guda goma wadanda suka karya kofar suka dauke su zuwa gidan Faruku Musa.
Ya ce lallai sun soki gwamnati ta hanyar wakokinsu saboda suna ganin wajibinsu ne a matsayinsu na ‘yan jihar na yin Allah wadai da abin da bai dace ba da ke gudana a jihar.
“Gaskiya ne mun soki gwamnati; a matsayinmu na masu kade-kade da raye-rayen waka a jihar Kebbi, mun dauki nauyin da ya rataya a wuyanmu na yin Allah wadai da mummunan shugabanci kuma hakan daidai ne abin da muka yi a daya daga cikin wakokin mu” in ji bayanin Arzilala da Sahara Reporters.
Kalli Hotunan su a kasa;
“Mun gaza ga iya yin shuru a yayin da Gwamna Bagudu ke ci gaba da lalata jiharmu ta hanyar shugabanci mara kyau. Amma ba mu taba tunanin cewa abi zai iya tayar da hankali ba.
“Da aka isar da mu a cikin dakinsa, ya umarci wasu mutane masu kwazo da karfin gaske da su doke mu har sai mun bayyana wanda ya aikemu don sukar gwamnan da wakokinmu.”
“A zahiri, ya zare bindiga AK47 da barazanar kashe Bello Aljanare. Bayan haka, ya gargade mu da kada mu kara bata sunan gwamna ko wani jami’in Gwamnatin Jihar Kebbi kafin a sake mu.”
A yanzu haka dai wadanda aka yiwa dukar suna karban kulawa da jinya a asibiti.
Darakta Janar na Kebbi Concern Citizens, wata kungiyar fararen hula, Ibrahim Mohammed, ya tabbatar da ziyartar wadanda suka jikkata a asibiti.