Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Nada Sabbin Sakatarorin Dindindin – Kalli Sunayansu

Published

on

at

Buhari Signing Minimum Wage Bill, Naija News Hausa, Hausa News, Labaran Hausa daga Naija News
advertisement

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da matar Ministan kwadago da aiki, Dr (Misis) Evelyn Ngige da wasu mutane takwas a matsayin sabbin Sakatarorin Dindindin a ranar Laraba.

Wannan sanarwar ya fito ne daga hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan farar hula na tarayya (Ag. HoCSF), Dr. Folashade Yemi-Esan.

Yemi-Esan ya sanar da cewa Shugaba Buhari ya amince da nadin Sakatariyar dindindin a yau Laraba, 18 ga watan Disamba 2019.

Bikin rantsar da su kuma ya gudana ne gabanin taron mako da mako na majalisar zartarwa na tarayya, wanda aka gudanar a zauren majalisa na fadar Shugaban kasa.

Sauran sabbin Sakatarorin da aka rantsar din sune: Engr. Hassan Musa daga Borno; Aliyu Ahmed daga Nijar; Olusola Idowu daga Ogun.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Leah Sharibu ta saura da rai, bisa bayanin Malamin Jami’a da aka sace.

Bitrus Bwala, wanda ya bayyana kansa a matsayin babban malami a Kwalejin Ilimi ta Gashua, a cikin jihar Yobe, a cikin wani faifan bidiyo da Ahmed Salkida, dan jaridar da aka sani da samun damar samun liki da kungiyar Boko Haram, ya bayyana cewa ya shaida da kisan ma’aikatan hudu da ‘yan kungiyar suka yi kwanan nan a Borno.