Labaran Najeriya
Shugaba Buhari ya Sanya Hannu a kan Kasafin Kudi na shekarar 2020
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 17 ga watan Disamba 2019, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 a cikin doka.
Naija News ta samu fahimtar cewa shugaban ya yi rattaba hannu ne ga kasafin kudi Naira miliyan 10.5 a ofishin fadar Shugaban kasa, Abuja.
Sanya hannu kan dokar kasafin kudin ya gudana ne a gaban Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattijai, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, a kuma gaban sauran manyan hafsoshin ma’aikatar tarayya. kamar yadda yake kunshe a cikin kudurin da Buhari ya gabatar a ranar 8 ga Oktoba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bada tabbacin sanya hannun a sashin kafafen sadarwa na Twitter da shugaban ke amfani da ita, @MBuhari.
Ga sakon Buhari a kasa a turance;
It is my pleasant duty, today, on my 77th birthday, to sign the 2020 Appropriation Bill into law. I’m pleased that the National Assembly has expeditiously passed this Bill. Our Federal Budget is now restored to a January-December implementation cycle.
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) December 17, 2019