Connect with us

Labaran Najeriya

An Tsige Shugaba Kasar Amurka Donald Trump – Karanta Dalili

Published

on

Majalisar Wakilan Amurka ta gurfanar da Shugaban Amurka Donald Trump saboda cin zarafin iko da toshewar Majalisa.

Naija News ta ba da rahoton cewa, Majalisar Wakilai ta tsige Trump a daidai karfe 8:23 na yamma a ranar Laraba bayan wata muhawara mai zafi da jefa kuri’un kan wasu zance biyu da aka wallafa na tsige shi bayan makonni na shaidar alaka da huldarsa da Ukraine.

A wata labarai, an tono wata faifan bidiyo da aka gano a kan yanar gizo, wadda ta bayyana wani Annabci da wani babban Annabi a Najeriya da kuma babban Fasto na Ikilisiyar Synagogue of All Nations, TB Joshua yayi da cewa za a jefa kuri’ar rashin amincewa’ kan Shugaban Amurka, Donald Trump.

A ranar 6 ga Nuwamba 2016, ‘yan kwanaki kafin zaben Amurka wanda Shugaba Donald Trump ya yi nasara, TB Joshua ya yi hasashen cewa wanda ya lashe zaben Amurka zai fuskanci kalubale, gami da’ kuri’ar rashin amincewa.

KARANTA WANNAN KUMA; Ban Gamsu Da Tsarin Dimokradiyya Ba – inji Shugaba Buhari