Connect with us

Labaran Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Kiristimati

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ayyana ranar 25 ga Disamba, 26th da Janairu 1, 2020 a matsayin ranar hutun jama’a don Kirsimeti, Ranar Dambe da kuma Sabuwar Shekara.

An sanrar da hakan ne ta hannun Ministan yada labarai na kasar, Rauf Aregbesola a ranar alhamis, ta hanyar wata sanarwa da sakatare-janar na ma’aikatar cikin gida, Georgina Ehuriah ta fitar.

Da yake magana a madadin gwamnatin shugaba Buhari, Aregbesola ya taya Kiristoci da dukkan ‘yan Najeriya a gida da kasar waje murna a yayin da bukin Kirsimeti ta 2019 da bukin Sabuwar Shekarar 2020 ke gabatowa.

Ya bukaci kiristoci suyi rayuwa mai kyau ta yin koyi da kyawawan dabi’u da koyarwar Yesu Kristi wadanda suka dangana da tausayi, hakuri, zaman lafiya, kaskantar da kai, adalci da kaunar juna.

Tsohon gwamnan jihar Osun din ya nuna gamsuwarsa da cewa shekarar 2020 zai zama shekarar nasara da ci gaba ga dukkan ‘yan Najeriya.

Ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya, a karkashin jagoranci shugaba Muhammadu Buhari, za ta tabbatar da ganin cewa ‘yan kasan dukka sun sami rayuwa mai dacewa.

Aregbesola ya yiwa ‘yan Najeriya fatan alheri da kwanciyar hankali a bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

KARANTA WANNAN KUMA; Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Sanar Da Shirinta Na Gina Masallacin Juma’a 90.